Zargin $16bn: Ku Bincike Ni Idan Akwai Hujjar Na Yi Sata — Atiku Ga Tinubu


 

Zargin $16bn: Ku Bincike Ni Idan Akwai Hujjar Na Yi Sata — Atiku Ga Tinubu


Umar Nusaiba Ibrahim 


Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta fito da kwararan hujjoji kan zarge-zargen da ake masa na almundahana, maimakon ci gaba da maimaita tsoffin zarge-zarge.


Atiku ya musanta cewa ya taɓa jagorantar aiwatar da aikin wutar lantarki da aka kashe dala biliyan 16, yana mai cewa Majalisar Tarayya ta taɓa binciken kwangilolin, amma ba a taɓa gayyatar sa domin ya amsa wani zargi ba.


Ya ce a matsayinsa na Mataimakin Shugaban Ƙasa ya jagoranci kwamitin sayar da kadarorin gwamnati, amma ba shi ne ya jagoranci aiwatar da kwangilolin wutar lantarkin ba. Ya kuma musanta hannu a harkar gwanjon kamfanin Aluminium Smelter.


Atiku ya ce idan akwai hujjar cewa ya wawure dukiyar ƙasa, gwamnati ta bincike shi, ta gayyace shi sannan ta gurfanar da shi a gaban kotu. Ya ce tun bayan da ya bar ofis a shekarar 2007, babu wata gwamnati da ta kai shi kotu kan irin waɗannan zarge-zarge.


A cewarsa, maimaita zarge-zargen na neman karkatar da hankalin ’yan Najeriya daga matsin tattalin arziki da suke fuskanta, musamman bayan cire tallafin man fetur a 2023.


A wani ɓangare kuma, Atiku ya gabatar da wani sabon tsari da ya ce zai rage farashin man fetur tare da sauƙaƙa wa ’yan Najeriya radadin tsadar rayuwa idan aka zaɓe shi a 2027.


#AtikuAbubakar #BolaTinubu #Zargin16Billion #NigeriaPolitics #2027Election #ADC #FuelSubsidy #NigerianPolitics #Tinubu #Atiku #NexviewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill