*Hisbah ta hana sana'ar turin fim, Abba yace a'a*
*Hisbah ta hana sana'ar turin fim, Abba yace a'a*
_Kabir Garba Hassan_
Hukumar tace finafinai da ɗab'i ta jahar Kano tace duk da tana sane da faifan murya da ake ta yaɗawa wadda ke ɗauke da saƙo na batsa, amma babu wata hukuma da ta tuntuɓeta kafin fitar da sanarwar dokar hana turin fim a waya.
Hukumar ta jaddada cewa lallai ta tura jami"anta ƙananan hukumomi 44 na Kano don bincike.
Wannan na zuwa ne Jim kaɗan bayan da wata sanarwa ta fito daga Hisba kan cewar an haramta sana'ar turin fim.
Wannan sabuwar sanarwa dai tana alamta tirka-tirka tareda cin karo da juna a aiki tsakanin Hisbah da Hukumar tace fina finai kan wannan batu.
To wanne za'abi? Ku bayyana mana ra'ayoyinku

Comments
Post a Comment