HISBAH TA HARAMTA SANA'AR TURA FIM A WAYA


 HISBAH TA HARAMTA SANA'AR TURA FIM A WAYA


Hukumar Hisbah ta Kano ta fita da sanarwar haramta sana'ar tura film a waya a faɗin jihar Kano.


Premier Radio ce ta ruwaito wannan labarin inda ta wallafa a shafinta na Facebook da safiyar yau Alhamis.


A cikin sanarwar an ruwaito cewa mataimakin babban kwamandan Hisbah Mallam Mujahiddeen shine ya aike da saƙon haramcin ga kafofin yaɗa labarai inda sanarwar ta ƙara da cewa Hisbah ta sha alwashin hukunta dukkan Wanda aka samu da saɓa wannan sabuwar doka.


Sana'ar tura film a waya dai tayi shuhura a kano musamman a yankunan karkara da kuma ƙananan unguwannin cikin birni.


Kabir Garba Hassan

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill