Matashi Mai Shekara 18 Ya Zama Farfesa Mafi Ƙanƙanta a Duniya


 

Matashi Mai Shekara 18 Ya Zama Farfesa Mafi Ƙanƙanta a Duniya 


By

Umar Nusaiba Ibrahim


Matashin Ba’amurke, Nathan Thomas, ya kafa sabon tarihi bayan ya zama farfesa mafi ƙarancin shekaru a duniya yana da shekara 18 kacal.


An naɗa shi malami a Miami Dade College a watan Agustan 2023 yana da shekara 18 da kwana 346, lamarin da ya karya tarihin da ya shafe sama da shekaru 300 yana hannun wani masanin lissafi ɗan Scotland.


Thomas ya fara karatu tun yana ɗan shekara 10, sannan ya samu digirin farko da na biyu a fannin injiniyan lantarki kafin ya cika shekara 19.


A cewarsa, koyarwa tana taimaka masa wajen ƙara fahimtar darussa, kuma burinsa shi ne taimaka wa ɗalibai su yi nasara.


A halin yanzu yana karantar da darussa ta intanet tare da karatun digirin lauya a University of Miami School of Law, inda ake sa ran zai kammala a shekarar 2028.


Duk da irin nasarorin da ya samu, Thomas ya ce yana rayuwar matashi kamar kowa, yana sha’awar wasannin ƙwallon kwando, tennis da golf, tare da ba da shawarar mutane su guji kwatanta rayuwarsu da ta wasu, su ci gaba da jajircewa domin samun nasara.


#NathanThomas

#YoungestProfessor

#WorldRecord

#Education

#Inspiration

#STEM

#Engineering

#HigherEducation

#SuccessStory

#BreakingBarriers

#NexviewTV

#WorldNews

#NewsUpdate

#DailyNews

#EducationNews

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill