TETFund Ta Dakatar da Sabbin Tallafi Ga Makarantun Da Suka Gaza Kammala Ayyukansu By


 

TETFund Ta Dakatar da Sabbin Tallafi Ga Makarantun Da Suka Gaza Kammala Ayyukansu


By 

Umar Nusaiba Ibrahim 

Hukumar TETFund ta sanar da cewa daga zagayen tallafin shekarar 2027, ba za ta amince da sabbin ayyuka ga jami’o’i, kwalejoji da sauran cibiyoyin ilimi da ke da ayyukan TETFund da ba a kammala ba ko aka yi watsi da su ba.


Shugaban Kwamitin Amintattu na TETFund, Aminu Masari, ya ce matakin na da nufin magance yawan jinkirin kammala ayyukan da asusun ke ɗaukar nauyi. Ya bayyana cewa dole ne cibiyoyin da abin ya shafa su kammala tsofaffin ayyukansu kafin su samu damar cin gajiyar sabbin tallafi.


Hukumar ta kuma umarci duk cibiyoyin da abin ya shafa su tattara jerin ayyukan da suka jinkirta fiye da watanni shida, su bayyana dalilan jinkirin tare da hanyoyin magance su. Haka kuma, ƙungiyoyin sa ido na TETFund za su gudanar da binciken zahiri a watan Agusta da Satumba na 2026 kafin a yanke hukuncin ayyukan da za su cancanci tallafin 2027.


#TETFund #Ilimi #JamioI #Polytechnic #CollegeOfEducation #Nigeria #TallafinIlimi #AyyukanGineGine #Bincike #NexviewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING