BUK Ta Haramta Cajin Baburan Lantarki Da Motocin Lantarki Masu Zaman Kansu A Harabar Jami’a
BUK Ta Haramta Cajin Baburan Lantarki Da Motocin Lantarki Masu Zaman Kansu A Harabar Jami’a
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta haramta cajin baburan lantarki da sauran motocin lantarki masu zaman kansu a dukkan harabobinta, sakamakon ƙaruwar kuɗin lantarki da jami’ar ke biya.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Lamara Garba, ya fitar, an bayyana cewa mahukuntan jami’ar sun lura da yadda ake amfani da wutar lantarkin jami’ar ba tare da ƙa’ida ba wajen cajin baburan lantarki da sauran motocin lantarki na masu zaman kansu.
Jami’ar ta ce wannan ɗabi’a ta taimaka wajen hauhawar kuɗin lantarki da take kashewa, lamarin da ke ƙara mata nauyin kuɗaɗe. Saboda haka, an haramta cajin irin waɗannan ababen hawa da wutar jami’ar nan take.
BUK ta umarci ma’aikata, ɗalibai, masu babur na kasuwanci da sauran masu amfani da baburan lantarki da su daina cajin ababen hawansu da wutar jami’ar. Ta kuma yi gargaɗin cewa duk wanda aka kama ya saɓa wa wannan umarni zai fuskanci hukuncin ladabtarwa bisa ƙa’idojin jami’ar.
Haka kuma, jami’ar ta umarci shugabannin kwalejoji, daraktoci, shugabannin sassa da na rassa da su sa ido kan bin wannan doka tare da kai rahoton duk wani wanda ya karya ta. Ta kuma ce za a riƙa sintiri a harabobin jami’ar domin tabbatar da bin umarnin.
#BUK #BayeroUniversity #Kano #Lantarki #ElectricVehicles #Ilimi #Najeriya #NexviewTV

Comments
Post a Comment