Huawei da NCCE Sun Kulla Yarjejeniya Don Faɗaɗa Ilimin AI da Fasahar Zamani a Najeriya


 


Huawei da NCCE Sun Kulla Yarjejeniya Don Faɗaɗa Ilimin AI da Fasahar Zamani a Najeriya


Daga Nusaiba Umar Ibrahim


Kamfanin Huawei Technologies Nigeria Limited da Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa (NCCE) sun rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa domin faɗaɗa koyar da Artificial Intelligence (AI) da inganta ilimin fasahar zamani a Najeriya.


An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a taron Huawei Education Summit 2026 da aka gudanar a Abuja.


Babbar Sakatariyar NCCE, Dr. Angela Ajala, ta ce haɗin gwiwar zai samar da Digital Academy domin horas da malamai da ɗalibai, yayin da hukumar ta ƙara darussa kamar AI, Robotics, Cybersecurity, Data Science da Software Development cikin tsarin karatu.


A nasa ɓangaren, Daraktan ICT na TETFund, Joseph Odo, ya bayyana cewa an ƙara tallafin ICT zuwa Naira miliyan 150 ga jami’o’i da Naira miliyan 100 ga kwalejojin ilimi da fasaha domin bunƙasa koyarwa, bincike da amfani da fasahar dijital.


An kuma karrama ɗalibai da jami’o’in Najeriya da suka yi fice a gasar Huawei ICT Competition 2025–2026 da aka gudanar a ƙasar Sin.



#Huawei #NCCE #AI #DigitalEducation #ICT #TETFund #Technology #Nigeria #NexviewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING