Hukumar ICPC Ta Bankado Yadda Hukumar Da Ba Ta Da Tushe Ta Shiga Kasafin 2026



 Hukumar ICPC Ta Bankado Yadda Hukumar Da Ba Ta Da Tushe Ta Shiga Kasafin 2026


Umar Nusaiba Ibrahim 


Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta bayyana cewa an shigar da wata hukumar da ba ta da ingantaccen tushe na doka cikin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2026, ba tare da an tabbatar da sahihancin kafuwarta ba.


Hukumar da ake kira PFIPC ta nemi a ware mata sama da Naira biliyan 3.85 domin biyan albashin ma’aikatanta. Daga bisani, an rage adadin zuwa Naira biliyan 1.3, wanda ya ƙunshi Naira miliyan 802 na albashi, Naira miliyan 200 na gudanar da ayyuka da kuma Naira miliyan 300 na manyan ayyuka.


A rahotonta na bincike, ICPC ta ce Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya bai gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa ba domin tabbatar da sahihancin takardun da aka gabatar da su a matsayin hujjar kafa hukumar. Maimakon haka, an dogara da wasu lambobin gudanarwa da takardu daga Ofishin Akanta-Janar na Tarayya da kuma Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.


Sai dai ICPC ta ce har yanzu ba ta samu wata shaida da ke nuna cewa an saki ko kashe Naira biliyan 1.3 da aka ware wa PFIPC ba. Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da bincike kan yadda hukumar ta samu shiga cikin tsarin kasafin kuɗin ƙasar.


A wani ɓangare kuma, Adeniyi Adeyemi, wanda ake danganta shi da lamarin, ya yi zargin cewa wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya sun amince da PFIPC ko kuma sun yi mu’amala da ita. Lauyoyinsa sun kuma buƙaci a ba shi damar bayyana a gaban kwamitin wucin-gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken lamarin.


Lauyoyin sun ce bai kamata a fitar da rahoton ƙarshe ba tare da an saurari Adeyemi ba, domin hakan na iya tauye masa damar kare kansa da kuma haƙƙinsa na samun adalci yayin binciken.


#ICPC #PFIPC #Kasafin2026 #Najeriya #Bincike #MajalisarWakilai #CinHanci #NigerianNews

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill