Hukumar Tace Fina-finai Ta Kulle Shagon Kausar Mai Back To Back Kan Zargin Tallan Da Ya Saɓa Wa Ɗabi’a
Hukumar Tace Fina-finai Ta Kulle Shagon Kausar Mai Back To Back Kan Zargin Tallan Da Ya Saɓa Wa Ɗabi’a
Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta rufe shagon Kausar Unique Empire Ltd, wadda aka fi sani da Kausar Mai Back To Back, bisa zargin amfani da kalamai da hotuna masu nuna batsa wajen tallata magungunan gargajiya a kafafen sada zumunta.
A cikin wata sanarwa da Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a madadin Shugaban Hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, an bayyana cewa sashen Ɗab’i mai kula da harkokin masu sayar da magungunan gargajiya ne ya ɗauki wannan mataki bayan samun bayanan sirri daga jama’a.
Sanarwar ta ce hukumar ta dade tana samun ƙorafe-ƙorafe daga al’umma kan irin yadda ake gudanar da tallan kayayyakin kamfanin, wanda ta ce ya saɓa wa ƙa’idojin tallata magungunan gargajiya da kuma kyawawan ɗabi’u da al’adun Jihar Kano.
Hukumar ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan doka kan duk wani da aka samu yana amfani da hanyoyin talla da suka saɓa wa dokokin da suka tanada.
A ƙarshe, ta yi kira ga masu gudanar da irin wannan kasuwanci da su tabbatar da cewa duk wani tallan da suke yi ya kasance cikin iyakokin doka tare da mutunta ƙa’idoji da al’adun al’umma.
#Kano
#KanoState
#Kannywood
#HukumarTaceFinaFinai
#KausarBackToBack
#MagungunanGargajiya
#SocialMedia
#DokarKano
#HausaNews
#Arewa
#NigeriaNews
#NexviewTV

Comments
Post a Comment