ICPC ta bankado wasu hukumomin bogi biyu a Najeriya


 


ICPC ta bankado wasu hukumomin bogi biyu a Najeriya


Daga Umar Nusaiba Ibrahim 


Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta ta Najeriya (ICPC) ta kammala binciken farko kan wata hukuma ta bogi mai suna Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC), inda ta gano cewa ba a kafa hukumar bisa wata doka, umarnin Shugaban Ƙasa ko wata sahihiyar takardar gwamnati ba. Binciken ya kuma tabbatar da cewa Adeniyi Adeyemi Mathew, wanda ya riƙa gabatar da kansa a matsayin Darakta-Janar na hukumar, bai samu sahihin naɗi daga gwamnatin tarayya ba.


Shugaban ICPC, Dr. Aliyu Musa, ya bayyana cewa an yi amfani da jabun takardun gwamnati wajen gudanar da ayyukan hukumar, ciki har da ƙirƙirar wasu hukumomi biyu na bogi, wato FCT Investment Promotion Agency (FIFA) da Foreign Investment Promotion Agency and Public-Private Partnership (FIFA-PPP). An kuma yi amfani da wasu takardun bogi wajen buɗe asusun bankunan waɗannan hukumomi.


ICPC ta ce binciken bai gano wata hujja da ke nuna cewa gwamnatin tarayya ta ware ko ta bai wa PFIPC kuɗaɗe ba. Sai dai hukumar ta gano cewa Adeyemi ya yi amfani da gibin da ke cikin tsarin tantance takardu da sa ido na wasu hukumomin gwamnati wajen gudanar da ayyukansa. ICPC ta kuma ce akwai alamun sakaci ko rashin kulawa daga wasu jami’an gwamnati.


A cikin shawarwarin rahoton wucin-gadin, ICPC ta ba da shawarar a gurfanar da Adeniyi Adeyemi a gaban kotu, tare da ɗaukar matakan ladabtarwa kan jami’an da aka samu da sakaci. Hukumar ta kuma ce tana ci gaba da binciken asusun bankunan PFIPC da na mutanen da ake zargin suna da hannu a lamarin. Wannan bincike na ICPC ya zo ne a daidai lokacin da Majalisar Wakilai ke gudanar da nata bincike kan badakalar.

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill