Jami’ar ABU Za Ta Fara Gudanar Da Digirin MBA A Fannin Gudanar da Ayyukan Hajji
Jami’ar ABU Za Ta Fara Gudanar Da Digirin MBA A Fannin Gudanar da Ayyukan Hajji
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya ta ƙulla yarjejeniyar haɗin gwiwa da Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) domin ƙaddamar da shirin Digirin Babbar Kwalin Gudanar da Kasuwanci (MBA) a Fannin Gudanar da Ayyukan Hajji.
An sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Juma’a a hedikwatar NAHCON da ke Abuja, inda aka bayyana cewa za a gudanar da shirin ta hannun Cibiyar Koyon Nesa ta Jami’ar ABU tare da haɗin gwiwar Cibiyar Nazarin Hajji ta Najeriya (HIN).
Sanarwar da Daraktan Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Auwalu Umar, ya fitar ta ce manufar haɗin gwiwar ita ce haɓaka ƙwarewa da inganta tsarin gudanar da aikin Hajji ta hanyar ilimi na musamman, horas da ƙwararru da kuma gudanar da bincike.
A cewar sanarwar, ɓangarorin biyu za su haɗa kai wajen tsara da sabunta manhajar karatu, gudanar da darussa kan Hajji da Umrah, shirya horaswa ga manyan jami’ai, gudanar da tarurrukan ƙwararru, samar da guraben koyon aiki da kuma bunƙasa bincike da ƙirƙire-ƙirƙire.
Bisa yarjejeniyar, Jami’ar ABU ce za ta kula da dukkan harkokin ilimi na shirin, ciki har da karɓar ɗalibai, samar da malamai, gudanar da jarrabawa da kuma bayar da Digirin MBA ga waɗanda suka cika sharuddan kammala karatu.
A nata ɓangaren, NAHCON za ta samar da ƙwararrun masana a fannin Hajji da Umrah domin koyarwa, tare da sauƙaƙa horas da ɗalibai a wuraren aiki da kuma samar musu da damar atisaye a Najeriya da ƙasashen waje.
Yarjejeniyar ta kuma tanadi bunƙasa bincike da ƙirƙire-ƙirƙire tare da tabbatar da kare haƙƙin mallakar fasaha da na marubuta da suka shafi ayyukan bincike na shirin.
Mataimakin Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Adamu Ahmed, ne ya sanya hannu a madadin jami’ar, yayin da Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya sanya hannu a madadin hukumar.
#ABU #NAHCON #MBA #GudanarDaHajji #Hajji #Umrah #Ilimi #JamiarABU #Nigeria #NexviewTV

Comments
Post a Comment