KASU Ta Roki ASUU Ta Dakatar da Yajin Aikin Gargadi
KASU Ta Roki ASUU Ta Dakatar da Yajin Aikin Gargadi
Umar Nusaiba Ibrahim
Shugabancin Jami’ar Jihar Kaduna, KASU, ya roƙi ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU reshen KASU da ta dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta fara.
Jami’ar ta ce matakin gwamnatin jihar na kafa kwamiti mai mambobi tara domin duba ƙorafe-ƙorafen malaman ya samar da wata dama ta warware matsalolin ta hanyar tattaunawa.
Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Musa, ya ce yajin aikin na iya yin illa ga ɗalibai da suka zo jami’ar daga sassa daban-daban na Kaduna da sauran jihohin ƙasar.
A cewar jami’ar, Gwamna Uba Sani ya kafa kwamitin da Kwamishinan Ilimi, Farfesa Abubakar Sani Sambo, ke jagoranta, domin tattaunawa da malaman tare da gabatar da shawarwari cikin wata guda.
ASUU-KASU ta fara yajin aikin ne bayan nuna rashin gamsuwa kan rashin aiwatar da wasu yarjejeniyoyi da kuma batutuwan da suka shafi jin daɗin malaman. Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan ficewar malaman jami’ar zuwa wasu wurare.
Sai dai jami’ar ta ce malaman ilimi 59 ne suka bar aiki tsakanin Janairu 2024 zuwa Agusta 2026, tana mai cewa tana ci gaba da tattaunawa da gwamnati da ƙungiyar domin kawo ƙarshen rikicin.
#KASU #ASUU #Kaduna #YajinAiki #JamiA #Education #NigeriaNews #NexviewTV

Comments
Post a Comment