Malaman Jami’o’i Sun Nemi A Samar Da Dokokin Amfani Da AI A Bincike Da Koyarwar Tarihi
Malaman Jami’o’i Sun Nemi A Samar Da Dokokin Amfani Da AI A Bincike Da Koyarwar Tarihi
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Malaman jami’o’i daga Najeriya da ƙasashen waje sun buƙaci a samar da ƙa’idoji da dokoki da za su tsara yadda ake amfani da fasahar Basirar Wucin Gadi (AI) a bincike da koyar da darasin tarihi a jami’o’i. Sun bayyana hakan ne a taron ƙasa da ƙasa da Sashen Tarihi na Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) ya shirya.
Sun ce duk da cewa AI na taimakawa wajen bincike ta hanyar sauƙaƙa nemo bayanai da tsara takardu, akwai haɗarin samun kuskuren bayanai, hujjojin bogi da son zuciya. Saboda haka, sun jaddada cewa dole ne a tantance duk bayanan da AI ya bayar kafin a yi amfani da su a ayyukan ilimi.
Mahalarta taron sun kuma buƙaci jami’o’i da ƙungiyoyin ƙwararru su samar da ƙa’idojin amfani da AI da suka shafi ɗa’a, kare bayanai, tabbatar da sahihancin bincike da bayyana inda aka yi amfani da AI. Haka kuma sun yi kira ga gwamnati da hukumomin ilimi su ƙarfafa koyar da darasin tarihi a dukkan matakan ilimi.
Bugu da ƙari, sun buƙaci a ƙara ƙoƙarin adana muhimman takardun tarihi, hotuna da bayanan gargajiya, tare da ƙarfafa masana tarihi su wayar da kan jama’a ta kafafen yaɗa labarai da dandamalin zamani. Sun kuma yi kira da a tallafa wa matasa masu bincike da kuma ci gaba da gudanar da irin waɗannan tarukan ilimi domin bunƙasa bincike da koyar da tarihi.
#Education #AI #ArtificialIntelligence #History #Universities #Research #OAU #HigherEducation #AcademicIntegrity #NexviewTV

Comments
Post a Comment