Matasa Sun Ƙona Motar Jami’an KAROTA Bayan Hatsari a Kano
Matasa Sun Ƙona Motar Jami’an KAROTA Bayan Hatsari a Kano
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Wasu fusatattun matasa sun ƙona wata motar aiki ta Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) bayan wani hatsari da ya faru a yankin Kwanar Dawaki da ke kan babbar hanyar Kano zuwa Zariya. Matasan sun zargi jami’an hukumar da haddasa hatsarin, lamarin da ya haifar da tashin hankali tare da ƙona motar.
Mataimakin Manajan-Daraktan KAROTA, Auwal Lawal Aranposu, ya ce hatsarin ya shafi wata motar Sharon da kuma wata tirela, inda tirelar ta buge motar Sharon har ta yi ta adungure sau da dama. Ya bayyana cewa jami’an KAROTA sun yi ƙoƙarin cafke direban tirelar, amma ya tsere daga wurin.
Aranposu ya ce wasu da ake zargin ɓata-gari ne suka kai wa jami’an KAROTA hari saboda sun yi zargin cewa su ne suka haddasa hatsarin, kafin daga bisani su banka wa motar aikin hukumar wuta. Ya musanta zargin da ake yi wa jami’an, yana mai cewa ba su da hannu a haddasa hatsarin.
Ya ƙara da cewa jami’an KAROTA sun taimaka wajen ceto waɗanda hatsarin ya shafa tare da kai su asibiti domin samun kulawar likitoci. Hukumar ta bukaci jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.
#Kano #KAROTA #Hatsari #KwanarDawaki #LabaranKasa #NexviewTV

Comments
Post a Comment