Najeriya Za Ta Fara Kera Motocin Yaƙi Da Na’urorin Yaƙi Da Jiragen Drone
Najeriya Za Ta Fara Kera Motocin Yaƙi Da Na’urorin Yaƙi Da Jiragen Drone
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Najeriya na ƙara ƙoƙarin samar da kayan aikin tsaro a cikin gida, yayin da Kamfanin Masana’antun Tsaro na Najeriya (DICON-D7G) ke shirin fara kera motocin yaƙi masu sulke, na’urorin dakile jirage marasa matuƙa da sauran kayan aikin soji na zamani.
Shirin na gudana ne tare da haɗin gwiwar kamfanin Eagles International for Defence Systems, domin musayar fasaha da ƙwarewa, samar da ayyukan yi da kuma rage dogaro da kayan aikin soji da ake shigo da su daga ƙasashen waje.
Babban Daraktan DICON-D7G, Osman Chennar, ya bayyana hakan bayan wata ziyarar da tawagar Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ta kai masana’antun kera kayan aikin soji a birnin Alƙahira na ƙasar Masar.
Ya ce haɗin gwiwar zai samar da ayyukan yi ga sama da mutane 200, ciki har da kusan tsofaffin jami’an soji 100 da suka yi ritaya. Haka kuma, Najeriya za ta samu damar koyon sabbin fasahohin kera kayan aikin tsaro.
Daga cikin motocin da ake shirin samarwa akwai motocin yaƙi masu sulke, motocin ɗaukar dakaru, motocin ɗaukar marasa lafiya da waɗanda suka samu raunuka daga fagen daga, da kuma motocin da ke da kariya daga hare-haren jirage marasa matuƙa da rokoki. Najeriya na kuma fatan samun damar sayar da wasu daga cikin kayayyakin ga sauran ƙasashen Afirka.
#Najeriya #DICON #Tsaro #SojojinNajeriya #KayanAikinSoji #MotocinYaki #Drone #FasaharSoji #Masanaantu #TsaronKasa #NigeriaDefence #DefenceIndustry

Comments
Post a Comment