NBTE Ta Amince Da Shirye-shiryen Karatu 10 A RECTEM
NBTE Ta Amince Da Shirye-shiryen Karatu 10 A RECTEM
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Najeriya (NBTE) ta amince da shirye-shiryen karatu guda 10 da Kwalejin Fasaha da Gudanarwa ta Redeemer’s (RECTEM) ke gudanarwa.
Cibiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, inda ta ce shirye-shiryen sun shafi fannonin fasahar gine-gine, gudanarwa da kuma kimiyya.
Daga cikin shirye-shiryen da aka amince da su akwai Architectural Technology, Estate Management and Valuation, Quantity Surveying, Accountancy, Business Administration and Management, Computer Science a matakan ND da HND, da kuma Science Laboratory Technology mai zaɓuɓɓuka uku.
RECTEM ta ce amincewar za ta ƙara mata ƙarfi wajen samar da ɗaliban da ke da ilimin aiki da ƙwarewar fasaha da ake buƙata a kasuwar ƙwadago.
Rector ɗin RECTEM, Dakta Oladunni Izobo-Martins, ta bayyana amincewar a matsayin wata babbar nasara ga cibiyar, tare da yabawa shugabanni, ma’aikata, ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudunmawar da suka bayar wajen cimma wannan nasara.
Ta kuma tabbatar da cewa RECTEM za ta ci gaba da inganta shirye-shiryenta domin bai wa ɗalibai ilimi da ƙwarewar aiki da za su ba su damar bayar da gudunmawa wajen ci gaban Najeriya.
#NBTE #RECTEM #Education #NigeriaEducation #TechnicalEducation #NexviewTV

Comments
Post a Comment