NELFUND Ta Bayyana An Bai Wa Dalibai Lamunin Naira Biliyan 322


 

NELFUND Ta Bayyana An Bai Wa Dalibai Lamunin Naira Biliyan 322


Umar Nusaiba Ibrahim 


Asusun Bayar da Lamunin Ilimi na Najeriya, NELFUND, ya ce ya raba sama da Naira biliyan 322 a matsayin lamunin karatu ga dalibai tun fara shirin.


Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyer, ya bayyana hakan a Uyo yayin wani shirin wayar da kan jama’a kan tsarin lamunin, inda ya ce cibiyoyin ilimi 319 da sama da dalibai miliyan 1.6 ne suka amfana da shirin zuwa yanzu.


Ya ce an samar da tsarin ne domin rage matsalolin kudi da ke hana daliban da suka cancanta samun damar ci gaba da karatunsu. A Jihar Akwa Ibom kuwa, NELFUND ta ce sama da dalibai 23,000 sun amfana, inda aka zuba kusan Naira biliyan 2.1 a jihar.


Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya ce gwamnatin jihar na tallafa wa dalibai ta hanyar biyan kudaden karatu da bayar da tallafin karatu. Ya ce kwanan nan jihar ta fitar da Naira biliyan 1.3, tare da kara tallafin kowane dalibi daga Naira 20,000 zuwa Naira 50,000.


Gwamnan ya kuma ce gwamnatin jihar na aiwatar da wasu shirye-shiryen bunkasa ilimi, ciki har da gina makarantun firamare da sakandare na zamani, tare da fadada shirye-shiryen karatu a manyan makarantunta.


Shugaban Jami’ar Uyo, Farfesa Christopher Ekong, ya yabawa kwamitin Majalisar Dattawa kan manyan makarantu bisa kawo shirin wayar da kan jama’a jami’ar, yana mai fatan hakan zai kara taimaka wa dalibai wajen samun damar karatu.


#NELFUND #Education #StudentLoan #Nigeria #Ilimi #Dalibai #NigerianEducation #AkwaIbom #Tinubu #NexviewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill