NERC Ta Sauke Daraktocin Kaduna Electric Kan Rashin Inganta Ayyuka
NERC Ta Sauke Daraktocin Kaduna Electric Kan Rashin Inganta Ayyuka
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta sauke dukkan daraktocin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (Kaduna Electric) daga mukamansu, bisa gazawar kamfanin wajen cika wasu daga cikin muhimman wajibcinsa da kuma inganta ayyukansa.
NERC ta bayyana cewa bashin da Kaduna Electric ke bin kasuwar wutar lantarki ya kai kusan Naira biliyan 456.5, yayin da kamfanin ya kuma ƙara tara wani sabon bashi da ya haura Naira biliyan 118.6 tun bayan da ASI Engineering Limited ta karɓi ragamar gudanar da kamfanin a shekarar 2024.
Hukumar ta ƙara da cewa kamfanin ya yi asarar kashi 71.88 cikin 100 na makamashin da ya karɓa da kuma kuɗaɗen da ya kamata ya tara a shekarar 2025.
NERC ta ce gazawar Kaduna Electric wajen cika wasu muhimman wajibcinta ce ta sanya ta ɗauki matakin sauke daraktocin kamfanin, tare da kafa kwamitin riƙon ƙwarya na tsawon watanni shida domin gudanar da harkokin kamfanin.
Kwamitin riƙon ƙwaryar zai kula da ayyukan kamfanin a lokacin da ake ɗaukar matakan da suka dace domin inganta ayyukansa tare da magance matsalolin kuɗaɗen da suka dabaibaye kamfanin.
#NERC #KadunaElectric #WutarLantarki #Nigeria #Labarai #HarkarWutarLantarki #NigerianElectricity #ElectricityDistribution #Kaduna #NERCNigeria

Comments
Post a Comment