Teach For Nigeria Ta Ƙara Sabbin Shugabannin Ilimi 499 Cikin Ƙungiyarta
Teach For Nigeria Ta Ƙara Sabbin Shugabannin Ilimi 499 Cikin Ƙungiyarta
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Ƙungiyar Teach For Nigeria ta karɓi sabbin shugabannin ilimi 499 cikin ƙungiyar tsoffin mambobinta domin ci gaba da yaƙi da rashin daidaito a fannin ilimi da tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ingantaccen ilimi.
Waɗanda aka karrama sun haɗa da malamai da shugabannin makarantu da suka shafe shekaru biyu suna gudanar da ayyukan inganta ilimi a yankunan da ba su da isassun kayayyakin more rayuwa a jihohin Legas da Ogun. Ayyukansu sun haɗa da inganta karatu da lissafi, ilimin fasaha, horas da malamai, da ƙarfafa gwiwar ‘ya’ya mata.
Babbar Daraktar Teach For Nigeria, Molade Adeniyi, ta yabawa waɗanda suka kammala shirin, tana mai cewa sun nuna shugabanci na gaskiya ta hanyar sadaukar da kai wajen sauya rayuwar ɗalibai. Ta bayyana cewa sun aiwatar da ayyuka 271 da suka kai ga sama da ɗalibai 68,000 kai tsaye da kuma fiye da 100,000 a kaikaice.
Shi ma wanda ya kafa ƙungiyar, Ayodele Olajiga, ya buƙaci sabbin mambobin su ci gaba da kasancewa jagororin canji, yana mai cewa nasarar shugaba tana bayyana ne ta hanyar zaɓin da yake yi wajen taimaka wa yara su samu damar cimma burinsu.
#LabaranIlimi #TeachForNigeria #Education #IngantaccenIlimi #NexviewTV

Comments
Post a Comment