Tinubu Ya Amince da Ɗaukar Malaman PTA 3,252 Aiki Dindindin
Tinubu Ya Amince da Ɗaukar Malaman PTA 3,252 Aiki Dindindin
Daga Umar Nusaiba Ibrahim
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da fara tsarin ɗaukar malamai 3,252 na ƙungiyoyin Iyaye da Malamai (PTA) aiki a Hukumar Ma’aikatan Tarayya. Matakin na da nufin rage ƙarancin malamai a Kwalejojin Haɗin Kan Tarayya da inganta ingancin ilimi.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya ce za a bai wa waɗanda aka tantance daga cikin malaman PTA fifiko, inda da dama daga cikinsu suka shafe tsakanin shekara 10 zuwa 25 suna koyarwa a makarantun tarayya ba tare da samun aikin dindindin ba.
A cewarsa, an cimma wannan mataki ne bayan wani cikakken aikin tantancewa da kwamitin haɗin gwiwar ma’aikatun gwamnati ya gudanar, wanda ya tabbatar da cancantar malamai 3,252 a fannoni daban-daban na koyarwa da horaswar fasaha.
Alausa ya ce ɗaukar malaman aiki zai ƙarfafa tsarin ilimi, inganta yawan malamai a makarantu, tare da ba wa dubban malamai da suka yi dogon lokaci suna hidima damar shiga aikin gwamnati bisa gaskiya da adalci.
#LabaranIlimi #Tinubu #PTATeachers #FederalUnityColleges #Ma’aikatanTarayya #EducationInNigeria #NigerianEducation #NexviewTV

Comments
Post a Comment