Yayin Fara Kamfen: Tsadar Kuɗin Izinin Billboard Ta Jefa ‘Yan Takara Cikin Fargaba


 

Yayin Fara Kamfen: Tsadar Kuɗin Izinin Billboard Ta Jefa ‘Yan Takara Cikin Fargaba


Umar Nusaiba Ibrahim 


Yayin da aka fara kamfen ɗin zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar Laraba, ‘yan takara da jam’iyyun siyasa sun fara shirin amfani da hanyoyin tallata manufofinsu domin samun karɓuwa a wajen masu zaɓe gabanin zaɓen 2027. Hukumar INEC zuwa yanzu ta tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa 19 da za su fafata a zaɓen watan Janairun 2027. Hanyoyin yaƙin neman zaɓen sun haɗa da taruka, gangamin siyasa, fastoci, takardun talla, allunan talla wato billboards, da kuma tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai.


Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa tun kafin a fara kamfen a hukumance, musamman lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyu, an riga an fara ganin tituna da garuruwa cike da hotunan ‘yan siyasa da allunan tallarsu. Sai dai wasu gwamnatocin jihohi sun sake duba ƙa’idojin saka billboards tare da ƙara kuɗaɗen izini, lamarin da ‘yan adawa da wasu masana ke ganin ka iya zama wata hanya ta takaita damar ‘yan takarar adawa wajen bayyana kansu. A wasu jihohi, kuɗaɗen sun kai ɗaruruwan miliyoyin naira.


A Rivers, ana karɓar N75m daga ɗan takarar shugaban ƙasa da N50m daga ɗan takarar gwamna domin saka billboard. A Kogi, kuɗin ya kai N150m ga ɗan takarar shugaban ƙasa, N50m ga Sanata, N30m ga ɗan Majalisar Wakilai, N5m ga Majalisar Dokokin Jiha, N2m ga ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukuma, yayin da councillor zai biya N300,000. A Abia, kuɗin billboard na shugaban ƙasa ya kai N200m, yayin da na gwamna N150m. A Anambra, shugaban ƙasa zai biya N50m, Sanata N20m, Majalisar Wakilai N5m, sannan Majalisar Dokokin Jiha N1.5m. Haka kuma, Cross River na karɓar N150m ga shugaban ƙasa da N100m ga gwamna, yayin da a Enugu aka ruwaito kuɗin ya kai N150m.


Sai dai Kano ta bambanta da wasu daga cikin jihohin, inda kuɗin billboard ya kasance N1.15m, ba tare da bambance tsakanin na kamfen da na kasuwanci ba. Hukumar Kano State Signage and Advertisement Agency ta ce tana aiki ne da kamfanonin talla da APCON ta yi wa rajista, kuma ɗan siyasa zai biya kuɗin ta hannun kamfanin talla da ya nema. A Kaduna kuma, babu wani ƙayyadadden kuɗi tun farko; ana duba wurin da ake son saka billboard sannan a tantance kuɗin da ya dace. A Bauchi kuwa, hukumomi sun umurci jam’iyyu su cire fastoci da billboards daga kan fitilun titi, sandunan amfani da jama’a da manyan gadunan sama, yayin da wasu jam’iyyu suka zargi gwamnati da yin amfani da dokar ba bisa ƙa’ida ɗaya ba.


Jam’iyyun ADC da NDC sun yi Allah-wadai da abin da suka kira tsadar kuɗaɗen billboard, suna zargin wasu gwamnatocin jihohi da ƙoƙarin tauye damar jam’iyyun adawa. Farfesa Kamilu Sani Fage na Jami’ar Bayero Kano ya ce ko da yake gwamnati na iya samun kuɗaɗen shiga ta hanyar billboard, bai kamata a yi amfani da hakan wajen ƙirƙirar wani shinge na kuɗi da zai hana ‘yan adawa isar da saƙonsu ga masu zaɓe ba. Masana harkokin siyasa da sadarwa ma sun ce billboards na da muhimmanci saboda suna kasancewa a wurare na tsawon lokaci kuma suna ba ‘yan siyasa damar samun gani sosai. A gefe guda kuma, jam’iyyar APC ta ce kuɗaɗen da ake karɓa da sharuddan saka billboards alhakin gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi ne, ba na jam’iyyar ko gwamnatin tarayya ba.


Wani muhimmin batu da rahoton ya tabo shi ne iyakar kuɗin da ‘yan takara za su iya kashewa a kamfen. Sabuwar Electoral Act 2026 ta ƙara iyakar kuɗin kamfen na shugaban ƙasa daga N5bn zuwa N10bn, na gwamna daga N1bn zuwa N3bn, na Sanata zuwa N500m, na Majalisar Wakilai zuwa N250m, yayin da na Majalisar Dokokin Jiha ya koma N100m. Masanin shari’a Kehinde Oloje ya bayyana cewa Electoral Act ba ta fayyace takamaiman kuɗin saka billboard ba; jihohi da ƙananan hukumomi ne ke da ikon tsara wuraren saka su da kuɗaɗen izini. Sai dai dokar zaɓen ta haramta tallan siyasa a cikin sa’o’i 24 kafin zaɓe, tare da hana kalaman batanci, ƙiyayyar addini ko ƙabilanci a tallan siyasa.


#NexviewTV #Zaben2027 #Kamfen2027 #Billboard #SiyasarNigeria #INEC #YanTakara #APC #ADC #NDC #NigeriaPolitics #ElectoralAct2026

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

Opposition Lawmakers Protest As Reps Pass State Police Bill