2027: ADC Da NDC Ba Barazana Ba Ne Ga APC — Nentawe


 


2027: ADC Da NDC Ba Barazana Ba Ne Ga APC — Nentawe


Umar Nusaiba Ibrahim 


Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyun adawa ta ADC da NDC ba su zama wata babbar barazana ga APC ba a zaɓen 2027.


Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Maiduguri, Jihar Borno, bayan kammala taron APC na tsawon kwanaki uku, wanda manyan jami’an jam’iyyar suka halarta.


Ya ce APC ta samu nasara a zaɓukan cike gurbi da aka gudanar kwanan nan, inda jam’iyyar ta lashe huɗu daga cikin zaɓuka biyar.


Haka kuma, ya ce APC ce ta yi nasara a zaɓen da aka gudanar kwanan nan a Ƙaramar Hukumar Ganye ta Jihar Adamawa.


Shugaban APC ya ce sakamakon waɗannan zaɓuka ya nuna cewa jam’iyyar na da ƙarfi kuma a shirye take domin tunkarar zaɓen 2027.


A yayin taron, shugabannin jam’iyyar sun kuma duba tsarin tafiyar da APC daga matakin ƙasa har zuwa rumfunan zaɓe. Sun yanke shawarar ƙara ƙarfafa sulhu da haɗin kan ’ya’yan jam’iyyar, tare da inganta ayyukan yaƙin neman zaɓe.


Taron ya kuma bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin Shugaba Kashim Shettima da sauran ’yan takarar APC da suka samu tikitin jam’iyyar.


A cewar jadawalin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a ranar 16 ga watan Janairu.


#APC #ADC #NDC #2027Elections #2027Zabe #NentaweYilwatda #BolaTinubu #KashimShettima #INEC #NigeriaPolitics #SiyasarNigeria #Zaben2027 #Maiduguri #Borno #Adamawa #Ganye #NexViewTV #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #DailyTrust



Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING