2027: INEC Ta Fitar da Jerin Ƙarshe na ‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa
2027: INEC Ta Fitar da Jerin Ƙarshe na ‘Yan Takarar Shugaban Ƙasa
Umar Nusaiba Ibrahim
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jerin ƙarshe na ‘yan takarar kujerar shugaban ƙasa da mataimakansu da za su fafata a babban zaɓen ƙasar da aka shirya gudanarwa a watan Janairun 2027.
Sakataren Hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ce ta sanya hannu kan jerin sunayen, wanda aka fitar ranar Asabar a Abuja. Jerin ya ƙunshi ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa 18 suka tsayar domin neman shugabancin ƙasar.
A cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa 18 da aka bayyana, maza su ne 16, wanda ke wakiltar kashi 88.9 cikin 100, yayin da mata biyu ne kacal, wato kashi 11.1 cikin 100.
Daga cikin fitattun ‘yan takarar maza akwai Bola Tinubu na APC, Abubakar Atiku na ADC, Peter Obi na NDC, Adewole Adebayo na SDP, Oluseyi Makinde na APM, Donald Duke na PRP, Chibuzor Okereke na LP da Omoyele Sowore na AAC.
A bangaren mata kuwa, Okwori Fredrick na NDP da Dr Esther Okereke na NRM ne aka bayyana a matsayin ‘yan takarar shugaban ƙasa mata biyu. Haka kuma, cikin mataimakan shugaban ƙasa 18, maza 14 ne, yayin da mata hudu ne.
INEC ta kuma fitar da jerin ƙarshe na ‘yan takarar kujerun Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai da za su fafata a zaɓen 2027.
#INEC #2027Election #Zaben2027 #NigeriaElection #ShugabanKasa #PresidentialElection #APC #ADC #NDC #SDP #LP #AAC #NigerianPolitics #NexViewTV
#Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa

Comments
Post a Comment