2027: Jam’iyyu Sun Shiga Fagen Yaƙin Neman Zaɓen Jihohi
2027: Jam’iyyu Sun Shiga Fagen Yaƙin Neman Zaɓen Jihohi
Umar Nusaiba Ibrahim
Yaƙin neman zaɓen kujerun gwamna da ’yan majalisun dokokin jihohi na zaɓen shekarar 2027 ya fara a jiya, Talata 8 ga Satumba, kamar yadda jadawalin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ya tanada.
Jadawalin INEC ya nuna cewa yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ’yan majalisar tarayya ya fara tun ranar 19 ga Agusta. Yanzu kuma an buɗe damar da ’yan takarar gwamna da ’yan majalisun jihohi za su fara gabatar da manufofinsu ga al’umma ta hanyar taruka, kafafen yaɗa labarai da sauran hanyoyin sadarwa.
Jam’iyyun siyasa da suka haɗa da APC, NDC da ADC sun tsayar da ’yan takarar gwamna a jihohi 28 da za a gudanar da zaɓen gwamna a cikinsu. Sai dai wasu daga cikin manyan jam’iyyun har yanzu ba su kammala kafa ko ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓensu ba.
A jam’iyyar APC, duk da cewa an sanar da sunayen mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen ƙasa, har yanzu ba a ƙaddamar da kwamitin a hukumance ba. Rahotanni sun ce ana sake duba wasu sunayen da aka saka cikin kwamitin sakamakon koke-koke da suka taso daga cikin jam’iyyar da kuma jama’a.
Haka kuma, jam’iyyun adawa da suka haɗa da NDC, ADC da PDP ba su ƙaddamar da wasu daga cikin manyan tsare-tsarensu da kwamitocin jihohinsu ba. Masana harkokin siyasa na ganin cewa rashin jituwar da ta biyo bayan zaɓen fidda gwani, matsalar kuɗaɗe da tattaunawar ƙulla ƙawance na daga cikin abubuwan da ke kawo tsaiko.
Yayin da wa’adin kwanaki 150 na yaƙin neman zaɓen kujerun jihohi ya fara, ana sa ran ayyukan siyasa za su ƙara ƙamari a makonni masu zuwa, yayin da jam’iyyu ke ƙoƙarin kammala shirye-shiryensu da kuma neman goyon bayan masu kaɗa kuri’a.
Sai dai zaɓen gwamna ba zai gudana a jihohin Imo, Ondo, Osun, Bayelsa, Edo, Kogi, Ekiti da Anambra ba, saboda jadawalin zaɓensu ya bambanta da na babban zaɓen shekarar 2027.
#2027Elections #Nigeria2027 #INEC #GovernorshipElection #StateAssembly #Election2027 #Campaign2027 #APC #ADC #NDC #PDP #NigeriaPolitics #HausaNews #NexviewTV #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #BBCHausa

Comments
Post a Comment