2027: Malaman Jami’o’in Arewa Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Tinubu
2027: Malaman Jami’o’in Arewa Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Tinubu
Umar Nusaiba Ibrahim
Fiye da manyan malaman jami’o’in gwamnati 600 daga jihohin Arewacin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Malamai daga jami’o’in gwamnati da dama na jihohin Arewa ne suka bayyana matsayar tasu a wani taro da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari, ya shirya domin tattauna makomar siyasar Najeriya. An gudanar da taron ne a cibiyar Umaru Musa Yar’Adua da ke Kaduna, inda aka gudanar da tattaunawar ne a bayan fage.
A cikin waɗanda suka halarci taron akwai gwamnan Kaduna, Uba Sani, gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, gwamnan Borno, Babagana Zulum, da takwaransa na Gombe, Inuwa Yahaya. Haka kuma, ministan tsaro Bello Matawalle, ministan gidaje Muttaqha Rabe Darma da tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, na daga cikin mahalarta taron.
Mataimakin shugaban jami’ar Jihar Kaduna, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, wanda ya karanta sanarwar ƙarshe ta taron, ya ce malaman sun duba ayyukan gwamnatin Tinubu tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023, tare da yin nazari kan yanayin tattalin arziki, siyasa, tsaro da zamantakewar al’umma, musamman a Arewacin ƙasar. Ya ce sun amince cewa gwamnatin ta gaji tattalin arzikin da ke fuskantar matsalolin kuɗaɗen gwamnati, tsarin kuɗi da sauran ƙalubale, tare da matsalar tsaro, ƙarancin ababen more rayuwa da gibin jarin ɗan Adam.
A cewar malaman, wasu daga cikin sauye-sauyen da gwamnatin ta aiwatar sun jawo ƙarin wahala ga jama’a, musamman ta fuskar tsadar rayuwa, sufuri da hauhawar farashin kayayyaki. Sai dai sun ce gwamnatin ta samu ci gaba a wasu fannoni da suka haɗa da samar da kuɗaɗen ilimi, noma, ababen more rayuwa, tallafawa ‘yan kasuwa, amfani da iskar gas wajen sufuri, jawo jarin masana’antu da bunƙasa tattalin arzikin dijital.
Bayan kammala tattaunawar, malaman sun bayyana goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027, amma suka jaddada cewa goyon bayan nasu ba “takardar amincewa marar iyaka” ba ne. Sun bukaci gwamnati ta saurari koken jama’a tare da magance matsalolin tsadar abinci da sufuri, rashin aikin yi da rashin tsaro.
Sai dai Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ya nesanta ƙungiyar daga wannan matsaya, yana mai cewa ASUU ƙungiya ce da ba ta shiga siyasar jam’iyya. Ya ce duk wani malami yana da ‘yancin shiga kowace jam’iyyar siyasa da yake so a matsayinsa na mutum, amma ASUU ba ta taɓa amincewa da wani ɗan takarar shugaban ƙasa ba, kuma ba za ta yi hakan ba.
A gefe guda, Ibrahim Masari ya ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki a Arewa domin neman goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027. A wani taro da ya yi da mata malaman addinin Musulunci daga jihohin Arewa 19, Masari ya ce wasu daga cikin ‘yan Arewa na adawa da Tinubu ne saboda ba Bahaushe ba ne kuma ba ɗan Arewa ba ne. Ya kuma kare tikitin takarar Shugaba da Mataimakin Shugaba na Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC, yana mai cewa abin da ya kamata ya zama ginshiƙin zaɓen shugabanni shi ne nagarta, ƙwarewa da tsoron Allah, ba ƙabila ba.
Masari ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa Tinubu zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda ya yi hasashen cewa za a ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a ranar 16 ga Janairu, 2027. A nasa ɓangaren, Gwamna Uba Sani ya ce matan malaman addinin sun goyi bayan Tinubu ne saboda irin nasarorin da suka ce ya samu da kuma yadda yake tafiyar da mulki, yana mai cewa za su isar da saƙon goyon bayansu zuwa al’ummomin jihohin Arewa 19
#Tinubu2027 #2027Election #NorthernNigeria #ASUU #NigeriaPolitics #NexViewTV #Arewa #SiyasarNigeria #BolaAhmedTinubu #Kaduna
#Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa

Comments
Post a Comment