2027: Zan Saukar Farashin Fetur Zuwa N200 Idan Aka Zaɓe Ni — Adebayo


 

2027: Zan Saukar Farashin Fetur Zuwa N200 Idan Aka Zaɓe Ni — Adebayo


Umar Nusaiba Ibrahim 


Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Prince Adewole Adebayo, ya yi alkawarin rage farashin man fetur, iskar gas na girki da man jiragen sama Jet A1 zuwa N200 kan kowanne lita, idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.


Adebayo ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da NAN a Abuja, inda ya ce za a iya cimma wannan buri cikin watanni 12 ta hanyar farfaɗo da matatun man Najeriya da kuma samar da yanayin da zai ba da damar ƙananan matatun mai (modular refineries) su bunƙasa.


Ya ce matatun man Najeriya har yanzu suna da amfani duk da cewa wasu sun kusa shekaru 50, yana mai cewa akwai matatun mai a Amurka da suka haura shekaru 100 amma har yanzu suna aiki. Ya kuma yi alkawarin dawo da tsarin tallafin man fetur na asali, wanda ke ware ganga 450,000 na ɗanyen mai domin amfanin cikin gida.


Dan takarar ya ce sauran kayayyakin da ake samu daga waɗannan gangar mai, kamar naphtha, diesel da kerosene, za a sayar da su, sannan a yi amfani da kuɗaɗen wajen daidaita farashin man fetur. Ya bayyana cewa muhawarar cire tallafin mai na ɗauke hankali daga muhimmin batun da ya shafi samar da isasshen man da ake tacewa a cikin gida.


Adebayo ya kuma yi alkawarin inganta harkokin sufuri da layin dogo domin rage dogaro da motocin haya masu zaman kansu. Ya ce a ƙarƙashin gwamnatinsa, kuɗin sufuri ba zai wuce kashi shida cikin ɗari na albashin ma’aikaci ba, yayin da kuɗin gidaje zai takaita zuwa kashi bakwai cikin ɗari. Ya kuma yi alkawarin samar da ilimi da kiwon lafiya kyauta da kuma mai da hankali kan noma domin tabbatar da Wadatar abinci 


#2027 #AdewoleAdebayo #SDP #Zaben2027 #FarashinFetur #ManFetur #N200 #Nigeria #Sufuri #TattalinArziki #Noma #Ilimi #KiwonLafiya #NAN #RFIHausa #ArewaRadio #Arewa24 #BBCHausa

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING