A hukumance, Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, wato FIFA, ta tabbatar da cewa shugabanta na yanzu, Gianni Infantino, zai sake tsayawa takarar shugabancin hukumar a zaɓe mai zuwa na shekarar dubu biyu da ashirin da bakwai (2027).

By Muhammad Ibraheem

Rahoton ya bayyana cewa, tun da fari ma dai Mista Infantino ya riga ya sanar da aniyarsa ta sake neman wannan babban kujera tun a watan Afrilun da ya gabata. Hukumar ta FIFA, ta sake nanata cewa babu abin da ya canza game da wannan shawara, kuma tabbas shugaban yana nan daram a kan bakarsa ta sake tsayawa takara don ci gaba da jagorantar ƙwallon ƙafa ta duniya.

Wannan mataki na Infantino ya nuna cewa yana son dorewar shirye-shirye da sauye-sauyen da ya kawo a cikin hukumar. Ko wane kalubale zai fuskanta a zaɓen na 2027? 

Kuma shin akwai wasu da ke shirin kalubalantarsa? Mu dai a nan, za mu ci gaba da sanya ido domin kawo muku yadda lamura za su kasance.

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING