Abu 4 da INEC ta haramta game da kamfe a wuraren ibada


 

Abu 4 da INEC ta haramta game da kamfe a wuraren ibada


Daga Zamira…


Yayin da jam’iyyun siyasa da ’yan takara ke ci gaba da shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na sauran mukamai a babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe a Najeriya, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, (INEC), ta sake jaddada wasu muhimman ƙa’idojin da suka shafi gudanar da kamfen na siyasa.


Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da dokokin zaɓen ƙasar suka tanada shi ne hana amfani da wuraren da aka ware domin ibada wajen gudanar da harkokin kamfen na siyasa.


A ƙarƙashin Sashe na 96 na Dokokin zabe wato (Electoral Act) 2026, wuraren ibada, ciki har da masallatai da coci-coci, ba za a yi amfani da su wajen gudanar da kamfen, gangamin siyasa ko jerin gwanon siyasa ba.


Bugu da ƙari, dokar ta hana amfani da waɗannan wurare wajen tallata, yaɗa ko kai hari ga wata jam’iyyar siyasa, ɗan takara, shirye-shiryensa ko manufofinsa.


Mun dubaDokokin zabe wato (Electoral Act) 2026 da kuma ƙa’idojin Hukumar zabe wato (INEC) na 2026, inda muka tattaro muhimman abubuwan da ya kamata ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki su sani game da wannan batu.


Na farko: Ba a yarda a gudanar da kamfen na siyasa a cikin wuraren da aka ware domin ibada ba. Wannan ya shafi masallatai, coci-coci da sauran wuraren ibada.


Na biyu: Ba a yarda a gudanar da gangamin siyasa ko jerin gwanon siyasa a irin waɗannan wurare ba. Dokar ta ware wuraren ibada daga wuraren da za a gudanar da irin waɗannan ayyukan siyasa.


Na uku: Ba a yarda a yi amfani da wurin ibada wajen tallata ko yaɗa wata jam’iyyar siyasa ko ɗan takara, ko kuma shirye-shiryensa da manufofinsa.


Na huɗu: Haka kuma, ba a yarda a yi amfani da wuraren ibada wajen kai hari ko suka ga wata jam’iyya, ɗan takara ko manufofinsa a matsayin wani ɓangare na harkar kamfen ba.


Na biyar: Dokar zaɓen ta kuma hana amfani da kalaman batanci, cin mutunci ko kalaman da za su iya tayar da hankali, musamman kalaman da za su iya cutar da ra’ayoyin addini, ƙabila ko wata ƙungiya a lokacin kamfen.


Hukumar zabe wato (INEC) ta kuma tanadi cewa yayin gudanar da gangami da kamfen, bai kamata a yi amfani da kalaman ƙiyayyawato(hate speech) ko kuma wani nau’in ƙarfi da tilastawa da zai iya haifar da rikici ba.


Manufar waɗannan ƙa’idoji ita ce taimakawa wajen tabbatar da cewa harkokin siyasa ba su mayar da wuraren ibada zuwa filin rikicin siyasa ba, tare da rage yiwuwar amfani da addini wajen rarrabuwar kawuna ko neman goyon bayan masu zaɓe.


Dokar ta zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, wanda tuni jam’iyyun siyasa da masu neman takara suka fara shirye-shiryen fafatawa a cikinsa.


Saboda haka, Hukumar zabe(INEC) na buƙatar jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu su fahimci ƙa’idojin da aka shimfiɗa domin gudanar da kamfen cikin lumana da bin doka.

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING