Adamawa: An Kama Malamin Makaranta Bisa Zargin Lalata da Yarinyar ’Yar Shekara 10


 

Adamawa: An Kama Malamin Makaranta Bisa Zargin Lalata da Yarinyar ’Yar Shekara 10


Samira Ahmad Danketa 


A ranar 26 ga Satumba 2026, ’yan sandan jihar Adamawa sun sanar da kama wani malamin makarantar firamare mai shekaru 54, mai suna Garba Suleiman, bisa zargin lalata da wata yarinya ’yar shekara 10.


Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ne ya bayyana hakan yayin da ake gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai.


Nguroje ya ce an kama malamin ne bayan iyalan yarinyar sun shigar da ƙorafi a hedikwatar ’yan sanda ta shiyyar Yola South. Ya bayyana cewa jami’an ’yan sanda sun gaggauta ɗaukar mataki tare da kama wanda ake zargin.


A cewar rundunar, binciken farko ya nuna cewa ana zargin malamin ya yaudari yarinyar sannan ya aikata lalata da ita. An kuma kai yarinyar asibiti domin yi mata gwajin lafiya.


Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Kabir Umar Hassan, ya bayar da umarnin tura lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) da ke Yola domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu. Kwamishinan ya kuma yi Allah-wadai da dukkan nau’o’in cin zarafin jinsi, tare da kira ga iyaye da masu kula da yara da su kasance cikin taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani mutum ko abu da suke zargi ga ’yan sanda.


#Adamawa #AdamawaNews #Police #NigeriaPolice #CrimeNews #ChildProtection #GBV #GenderBasedViolence #ChildAbuse #Justice #NigeriaNews #LabaranHausa #LabaranYau #NexviewTV

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING