Aisha Buhari Ta Kai Ziyara Ga Atiku Abubakar


 Aisha Buhari Ta Kai Ziyara Ga Atiku Abubakar


Umar Nusaiba Ibrahim 


Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta kai ziyara ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar. Atiku ne ya bayyana hakan ta kafafen sada zumunta, inda ya ce ya karɓi Aisha Buhari cikin farin ciki da girmamawa.


Atiku ya yi amfani da ziyarar wajen bayyana damuwarsa kan halin da al’ummar Najeriya ke ciki, musamman yadda tsadar abinci, sufuri, ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman abubuwan rayuwa ke ƙara matsa wa iyalai lamba.


Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce ‘yan Najeriya na buƙatar tattalin arzikin da zai bai wa masu aiki tuƙuru damar samun ci gaba, tare da dawo da damar samun ingantacciyar rayuwa. Ya ce burinsa shi ne gina Najeriya da za ta kasance mai amfani ga al’ummarta, tare da samar da mutunci, fata da damar samun rayuwa mai inganci ga kowane iyali.


Atiku ya ce ya ƙuduri aniyar rage wa ‘yan Najeriya nauyin da suke fuskanta, tare da dawo da fata da kuma mayar da Najeriya ƙasa mai sauƙin rayuwa. Ya bayyana cewa jin daɗin jama’a da makomarsu ya kamata su kasance cikin abubuwan da duk mai neman shugabanci zai ba fifiko.


Aisha Buhari, wadda ta kasance mai goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta je ziyarar ne tare da ɗaya daga cikin ‘ya’yanta mata da wasu makusanta. Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da ainihin dalilin ziyarar ko abin da aka tattauna tsakaninta da Atiku ba.



#NexViewTV #AishaBuhari #AtikuAbubakar #ADC #NigeriaPolitics #SiyasarNajeriya #Tinubu #2027Politics #Nigeria #Arewa #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING