An Ƙara Tsaurara Matakan Tsaro Yayin Ziyarar Shettima a Adamawa
An Ƙara Tsaurara Matakan Tsaro Yayin Ziyarar Shettima a Adamawa
Samira Ahmad Danketa
Rundunar ’yan sandan jihar Adamawa ta ƙara tsaurara matakan tsaro a babban birnin jihar gabanin ziyarar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda zai ziyarci jihar a yau Alhamis.
Ana sa ran Shettima zai jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa Adamawa domin jajanta wa gwamnatin jihar, Majalisar Masarautar Adamawa da kuma iyalan marigayi Alhaji Bamanga Tukur, wanda ya rasu ranar Asabar kuma aka binne shi ranar Lahadi a Yola.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana cewa Kwamishinan ’yan sanda, CP Kabir Umar Hassan, ya bayar da umarnin tura jami’an tsaro da dama domin tabbatar da tsaron ziyarar.
Daga cikin jami’an da aka tura akwai rundunar Police Mobile Force (PMF), Counter-Terrorism Unit (CTU), Anti-Kidnapping Unit, Intelligence Unit, Traffic Unit da kuma jami’an ’yan sanda na sassan jihar.
Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan tare da kai rahoton duk wani mutum ko motsi da ake zargi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kuma ta lambobin gaggawa na rundunar. A halin yanzu, gidan marigayi Bamanga Tukur ya zama cike da masu zuwa jajanta wa iyalansa da al’ummar jihar Adamawa bisa rasuwarsa yana da shekaru 90.
#Adamawa #KashimShettima #VicePresident #BamangaTukur #AdamawaNews #Yola #NigeriaNews #Security #Police #BreakingNews #HausaNews #NigerianNews #NexviewTV
Comments
Post a Comment