An Kashe Ƴan Najeriya Uku A Afirka Ta Kudu Cikin Kwanaki Hudu
An Kashe Ƴan Najeriya Uku A Afirka Ta Kudu Cikin Kwanaki Hudu
Umar Nusaiba Ibrahim
An kashe wasu ƴan Najeriya uku a wasu hare-hare daban-daban a ƙasar Afirka ta Kudu cikin kwanaki huɗu, lamarin da ya ƙara jawo damuwa kan tsaron ƴan Najeriya da ke zaune ko gudanar da harkokinsu a ƙasar.
Jakadan Najeriya da aka naɗa zuwa Afirka ta Kudu, Femi Fani-Kayode, ya bayyana cewa kisan ya faru ne a ranakun 18, 20 da 21 ga Satumba, 2026. Ya ce hakan ya kai adadin ƴan Najeriya da aka ce an kashe a Afirka ta Kudu a wannan shekarar zuwa 12, yayin da tun daga 2022 aka kashe mutum 112.
A cikin wata sanarwa, Fani-Kayode ya ce bayanan kashe-kashen sun isa gare shi ne daga ofishin Jakadan Najeriya a Johannesburg. Ya yi kira ga hukumomin Afirka ta Kudu da su gudanar da cikakken bincike, gano waɗanda ke da hannu da kuma gurfanar da su a gaban kotu, tare da ɗaukar matakan kare rayukan ƴan Najeriya.
Ofishin Jakadancin Najeriya a Johannesburg ya bayyana sunayen waɗanda suka mutu a matsayin Kenechukwu Christopher Igwemmadu, Olaniyi Olaleye Olatunde da Christian Hillary Nnaemeka. Ofishin ya ce Igwemmadu ya mutu ne a ranar 18 ga Satumba bayan da ake zargin ya yi tsalle daga wani bene yayin ƙoƙarin tserewa daga abin da ya bayyana a matsayin cin zarafin ‘yan sanda a Bloemfontein. Olatunde kuwa, wanda ke aiki a matsayin jami’in tsaro, an harbe shi a wani wurin shakatawa da ke Mamelodi East, Pretoria, bayan wata takaddama da wani kwastoma.
Dangane da Nnaemeka, ofishin jakadancin ya ce ya mutu ne bayan wani arangama da tawagar Sizok’thola, wadda Xolani Khumalo ke jagoranta, a Primrose da ke Ekurhuleni. Ofishin ya yi zargin cewa an ci zarafinsa tare da dukan sa yayin wani samame, kafin daga bisani ya yi ƙoƙarin tserewa, inda ya faɗi sakamakon raunuka da gajiya. An kai shi asibiti, amma aka tabbatar da mutuwarsa bayan isarsa.
Ofishin Jakadancin ya ce abubuwan da suka faru na da matuƙar tayar da hankali, tare da yin kira ga hukumomin Afirka ta Kudu da su gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu. Ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da ke ƙasar su kasance masu bin doka da oda, taka-tsantsan da kuma guje wa duk wani abu da zai iya jefa rayuwarsu cikin haɗari. A baya-bayan nan, hukumomin Najeriya sun sha yin kira ga Afirka ta Kudu da ta ƙara kare ƴan Najeriya daga kashe-kashe, hare-haren kyamar baƙi da sauran nau’o’in cin zarafi.
#NexViewTV #SouthAfrica #Nigeria #NigeriansInSouthAfrica #Arewa #ArewaNews #LabaranArewa #HausaNews #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #FreedomRadioKano #DailyTrust #Tsaro #NigeriansAbroad #LabaranKasa #LabaranDuniya

Comments
Post a Comment