An Sace Limaman Juma’a Shida Yayin Zuwa Addu’ar 2027
An Sace Limaman Juma’a Shida Yayin Zuwa Addu’ar 2027
Umar Nusaiba Ibrahim
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashin daji ne sun sace limaman Juma’a shida a jihar Zamfara, yayin da suke kan hanyar zuwa Talata Mafara domin halartar wata addu’a ta musamman da aka shirya domin neman zaman lafiya da kuma nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
An sace limaman ne kimanin kilomita uku daga ƙauyen Damri, a wani wuri da ake kira Gidan Suleiman Bature da ke dajin Gonar Sarkin. Addu’ar dai an shirya ta ne bisa gayyatar tsohon Gwamnan Zamfara kuma Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2027, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar.
Mazauna yankin sun bayyana cewa limaman da aka sace sun haɗa da Limamin Masallacin Juma’a na Dakko, Malam Shehu; Limamin Dogon Madacci, Liman Yahuza da mataimakinsa; Limamin Fagon, Liman Bala; da Limamin Tungar Nagodai, Na’ibi Tasi’u. Dukkansu daga ƙananan hukumomin Bakura da Anka ne.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kuma sace wasu mutane biyu da wani direba mai suna Abun Abu, yayin da suka sake mutum ɗaya bayan sun karɓi Naira miliyan 1.9 da yake ɗauke da su. Mazauna yankin sun ce matsalar tsaro ta sa mutane da dama a ƙauyukan da ke kusa da Damri sun kasa fita zuwa gonakinsu saboda fargabar sace su.
Wani mazaunin yankin ya ce wasu ƙauyuka da suka haɗa da Matsafa, Yar Matsafa, Gazamnah, Lambusu, Sabon Garin Damri, Kurhi, Mallamawa, Saturu da Cikayi, suna fuskantar barazanar ’yan bindiga, waɗanda ake zargin suna karɓar haraji daga manoma kafin su girbi amfanin gonakinsu.
Rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da sace limaman, inda kakakinta, DSP Yazid Abubakar, ya ce adadin limaman da aka sace shida ne. Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun ƙara kaimi wajen gudanar da aikin ceto domin ganin an dawo da su lafiya.
#Zamfara #Abduction #YanBindiga #Tsaro #LimamanJumaa #TalataMafara #Damri #Yari #Tinubu2027 #Zaben2027 #NigeriaSecurity #NigerianPolitics #NexViewTV #ArewaRadio #RFIHausa

Comments
Post a Comment