ASUU Ta Yi Barazanar Sake Yajin Aiki a Faɗin Ƙasa
ASUU Ta Yi Barazanar Sake Yajin Aiki a Faɗin Ƙasa
Umar Nusaiba Ibrahim
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta yi barazanar sake dawo da yajin aikin da ta dakatar a faɗin ƙasar, idan Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi suka gaza daukar matakan gaggawa kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi jin daɗin malaman jami’o’i.
ASUU ta ce za ta iya sake fara yajin aikin “ba tare da wani ƙarin sanarwa ba”, sakamakon gazawar kammala aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a watan Disamban 2025, da kuma rashin biyan ragowar albashin watanni uku da rabi daga cikin watanni bakwai da rabi da aka riƙe wa malaman jami’o’i. Haka kuma, ƙungiyar ta yi zargin cewa har yanzu ba a tura wasu kuɗaɗen da aka cire daga albashin malaman ba, waɗanda suka kai biliyoyin naira.
Shugaban ASUU na ƙasa, Christopher Piwuna, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar Juma’a, bayan wani taron gaggawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta ƙungiyar, wanda aka gudanar a Jami’ar Abuja. Ya ce yarjejeniyar Disamban 2025 ta biyo bayan shafe sama da shekaru takwas ana tattaunawa da gwagwarmaya, amma har yanzu Gwamnatin Tarayya da wasu gwamnatocin jihohi ba su aiwatar da ita gaba ɗaya ba.
Ƙungiyar ta yaba wa Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, da gwamnatocin Bauchi, Ekiti, Ogun, Benue, Yobe, Adamawa, Kebbi, Katsina da Borno, saboda fara aiwatar da yarjejeniyar. Ta kuma ce gwamnatocin Kano, Edo, Plateau, Taraba, Gombe da Bayelsa sun yi alƙawarin fara aiwatar da yarjejeniyar a watan Satumba ko Oktoba. Sai dai ASUU ta gargadi sauran jihohin da su gaggauta ɗaukar mataki domin kauce wa abin da ta kira “babbar matsalar aiki” a jami’o’in gwamnati.
Dangane da albashin da aka riƙe, ASUU ta ce ta yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa biyan watanni huɗu daga cikin watanni bakwai da rabi da aka riƙe a zamanin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Sai dai ta buƙaci a biya sauran watanni uku da rabi nan take. Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa kuɗaɗen fansho, na ƙungiyoyin haɗin gwiwa da kuma kuɗaɗen ƙungiyar kwadago da aka cire daga albashin malamai, waɗanda suka kai biliyoyin naira, ba a tura su zuwa wuraren da suka dace ba tsawon watanni.
ASUU ta ce matsalar biyan albashin da ba a biya ba, kuɗaɗen da ba a tura ba da kuma rashin cikakken aiwatar da yarjejeniyar na barazana ga zaman lafiyar masana’antu a jami’o’in ƙasar. Ta ƙara jaddada cewa idan ba a magance matsalolin cikin gaggawa ba, Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta ASUU na iya sake kunna yajin aikin da ta dakatar ba tare da wani ƙarin sanarwa ba.
#ASUU #YajinAiki #Jamiioi #MalamanJamiIoi #Ilimi #Albashi #GwamnatinTarayya #Nigeria #Education #University #AcademicStaff #NigerianUniversities #Tinubu #NexViewTV #BBCHausa #RFIHausa #Arewa24 #ArewaRadio

Comments
Post a Comment