Ba Ni Da Abin Ɓoyewa” — Obi Ya Nemi UNN Ta Bayyana Bayanan Karatunsa


 “Ba Ni Da Abin Ɓoyewa” — Obi Ya Nemi UNN Ta Bayyana Bayanan Karatunsa


Umar Nusaiba Ibrahim 


Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress, NDC, Peter Obi, ya buƙaci jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi da ya taɓa karatu a cikinsu su fito fili su bayyana bayanan karatunsa, yana mai cewa ba shi da wani abin da yake ɓoyewa.


Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin 90 Minutes Africa, inda yake martani kan ikirarin da jakadan Najeriya mai jiran aiki a Mexico, Reno Omokri, ya yi cewa ƴan takarar shugaban ƙasa a Najeriya suna da fayiloli a hannun Hukumar Binciken Laifuka ta Tarayya ta Amurka, FBI. Obi ya ce bai taɓa mu’amala da FBI ba, kuma bai san cewa yana da wani fayil a wurinta ba.


Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce duk wanda ke neman riƙe muƙamin gwamnati ya kamata ya kasance a shirye domin a binciki tarihinsa da bayanansa yadda ya kamata. Ya kuma roƙi Jami’ar Najeriya da ke Nsukka, UNN, da ta fitar da dukkan bayanan da ke cikin fayil ɗinsa, ciki har da takardun shigarsa jami’a da sakamakon karatunsa daga shekarar farko har zuwa kammala karatu.


Obi ya kuma nemi sauran cibiyoyin da ya halarci shirye-shiryen karatu na musamman da su bayyana bayanansa ga jama’a. Daga cikinsu akwai Lagos Business School, London School of Economics, Columbia Business School, Kellogg School of Management, Harvard Business School, da jami’o’in Oxford da Cambridge, da kuma INSEAD da IMD.


Ya ce bayyana gaskiya da kuma amincewa da binciken jama’a ya kamata su kasance daga cikin muhimman abubuwan da ake buƙata ga duk wanda ke neman riƙe muƙamin gwamnati. Obi ya ƙara da cewa shugabanni ya kamata su kasance abin koyi wajen bin ƙa’idojin gaskiya da riƙon amana da suke buƙata daga al’umma.


A gefe guda kuma, Obi ya ƙalubalanci sauran ƴan takarar shugaban ƙasa da su rungumi irin wannan mataki na buɗe bayanansu ga jama’a. Ya ce duk wani ɗan siyasa da ke da tarihin da ke haifar da tambayoyi ya kamata ya kasance a shirye ya yi wa al’ummar Najeriya bayani.


Batun sahihancin bayanan karatun Obi ya sake kunno kai a wannan kakar siyasa, bayan wani ɗan siyasa, Abayomi Arabambi, ya shigar da ƙara a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin kin fitar da bayanan karatun Obi da Jami’ar Najeriya, Nsukka, ta yi.


Arabambi ya ce ya nemi jami’ar ta ba shi kwafin takardar shaidar karatu da aka tabbatar da sahihancinta, wato Certified True Copy, CTC, mai lamba D000198, wadda ake cewa jami’ar ta bai wa Gregory Peter Onwubuasi Obi a shekarar 1984 bayan kammala karatun Digirin Falsafa, amma jami’ar ta ƙi amincewa da buƙatarsa.


A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/2144/2026, wadda aka shigar a ranar 9 ga Satumba, Arabambi ya ce ya aika wa jami’ar wasiƙa a ranar 16 ga Yuli, 2026, yana neman kwafin takardar shaidar da kuma bayanan karatun da aka dogara da su wajen bayar da wannan digiri.


Ya ce jami’ar ta karɓi buƙatar a ranar 6 ga Agusta, 2026, kuma an gabatar da ita ne bisa tanadin Dokar ‘Yancin Samun Bayanai ta shekarar 2011. Sai dai, a cewarsa, jami’ar ta kasa samar da bayanan da aka nema cikin lokacin da dokar ta tanada.


Arabambi ya kuma yi zargin cewa jami’ar ba ta aike masa da rubutacciyar sanarwar ƙin bayar da bayanan ba, tare da bayyana takamaiman sashe na dokar da ta dogara da shi wajen ƙin amincewa da buƙatarsa.

#PeterObi #UNN #NDC #NigeriaPolitics #2027Election #Obi #Politics #NigerianNews #NexViewTV #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING