Fashewar Ma’ajiyar Makamai a Syria Ta Hallaka Mutane 14
Fashewar Ma’ajiyar Makamai a Syria Ta Hallaka Mutane 14
Daga Zamira Ahmad Nasidi
Akalla mutane 14 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 11 suka jikkata sakamakon wata babbar fashewa da ta afku a wata ma’ajiyar makamai da kayayyakin yaƙi a kusa da birnin Sarmada, da ke lardin Idlib a arewa maso yammacin Syria.
Rahoton ya ce fashewar ta afku ne a ranar Laraba a wani wurin wucin-gadi da ake ajiye makamai da sauran kayayyakin yaƙi kafin a kwashe su zuwa wani wuri.
Ma’aikatar Tsaron Syria ta bayyana cewa wasu daga cikin jami’anta na cikin wadanda suka jikkata.
Bayan fashewar, gobara ta tashi a wurin tare da fitar da hayaki mai yawa, yayin da wasu ƙananan fashe-fashe da suka biyo baya suka kawo cikas ga aikin jami’an kashe gobara da masu aikin ceto.
Jami’an tsaro da ƙungiyoyin agaji sun garzaya wurin domin gudanar da aikin ceto tare da neman mutanen da ka iya kasancewa a ƙarƙashin baraguzan ginin. Haka kuma, an rufe wasu hanyoyin da ke kaiwa wurin domin kare lafiyar fararen hula.
Har zuwa yanzu, hukumomin Syria ba su bayyana ainihin abin da ya haddasa fashewar ba, yayin da bincike kan musabbabin lamarin ke ci gaba.
Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan wata makamanciyar fashewa da ta afku a Binnish, ita ma a lardin Idlib, inda mutane biyar suka mutu bayan wata mota dauke da harsasai ta fashe.
#Syria #Idlib #Sarmada #SyriaNews #Explosion #BreakingNews #WorldNews #MiddleEast #WarNews #NewsUpdate #InternationalNews #ZamiraTV #ZamiraNews #LabaranDuniya #LabaranKasaDuniya

Comments
Post a Comment