Firgici A Neja: ‘Yan Ta’adda Sun Sace Mutane 14 Daga Iyali Ɗaya


 

Firgici A Neja: ‘Yan Ta’adda Sun Sace Mutane 14 Daga Iyali Ɗaya


Umar Nusaiba Ibrahim 


Wata ɗaliba a Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Akram’s da ke Jihar Neja, Muhibbat Abass, ta bayyana cewa mutane 14 daga cikin iyalanta na hannun ‘yan ta’adda, bayan harin da aka kai kan masu ibada a wasu masallatan Juma’a guda huɗu a ƙaramar hukumar Borgu.


Muhibbat ta ce daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su akwai mahaifinta, kakanta, ‘yan uwanta da sauran danginta. Ta ce tun bayan faruwar lamarin ta dakatar da karatunta, sakamakon matsanancin tashin hankali da kuma rashin wanda zai ci gaba da daukar nauyin karatunta bayan an yi garkuwa da mahaifinta.


Harin ya faru ne a ranar 21 ga Agusta a garuruwan Dekara, Kpenya, Sabon-Gida da Gidan-Zana, lokacin da musulmi ke gudanar da sallar Juma’a. Bayan kwana biyu, ‘yan ta’addan sun fitar da wani bidiyo da ke nuna wasu daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da su, ciki har da mata da yara.


Al’ummomin da abin ya shafa sun ce adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ya haura 500, inda daga baya suka fitar da jerin sunayen mutane 547 da suka ce an sace. Wannan adadi ya sha bamban da bayanan da Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayar, wanda ya ce mutane 63 ne aka sace.


Haka kuma, wasu daga cikin iyalan waɗanda abin ya shafa sun bayyana cewa an kashe mutane da dama, an kona gidaje, tare da wawure kuɗaɗe, babura da sauran kayayyaki. Wani daga cikin mazauna yankin, Abdulkadir Idris, ya ce mahaifinsa yana cikin waɗanda aka sace, yayin da wasu ‘yan uwansa daga bangarorin mahaifinsa da mahaifiyarsa suka rasa rayukansu.


A gefe guda, gwamnatin Jihar Neja ta ce tana haɗa kai da jami’an tsaro domin ceto dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su. Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ma ta ce an tura ƙarin jami’an tsaro, rundunonin yaƙi da ta’addanci da kuma jirgin sama domin ƙarfafa aikin ceto. Sai dai iyalan waɗanda aka sace na ci gaba da kira ga gwamnati da ta gaggauta kuɓutar da ‘yan uwansu da ke hannun ‘yan ta’addan.



#NexViewTV #NigerState #Borgu #Arewa #ArewaNews #LabaranArewa #HausaNews #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #FreedomRadioKano #DailyTrust #Nigeria #Tsaro #GarkuwaDaMutane #YanTaAdda #LabaranKasa #LabaranDuniya

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING