FRSC: Ba a Bai wa Kowa Takardar Nadin Aiki ba a Daukar Ma’aikatan 2026
FRSC: Ba a Bai wa Kowa Takardar Nadin Aiki ba a Daukar Ma’aikatan 2026
Samira Ahmad Danketa
Hukumar Kula da Tsaron Hanyoyi ta Tarayya, FRSC, ta karyata wani labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke cewa Hon. Ali Isah, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Balanga/Billiri a Jihar Gombe, ya samo wa mutanen mazabarsa guraben aikin FRSC guda 50.
FRSC ta ce har yanzu ba a bai wa wani ɗan takara takardar nadin aiki ba a cikin aikin ɗaukar ma’aikatan shekarar 2026. Jami’in Ilimantar da Jama’a na hukumar, Osondu Ohaeri, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
Ya ce waɗanda suka yi nasara a matakan tantancewa da hira an gayyace su ne zuwa wuraren horo da FRSC Academy domin ci gaba da sauran matakai na ɗaukar aikin.
Hukumar ta bayyana cewa dole ne ‘yan takarar su kammala horo, tantancewa, regimentation da sauran matakan da aka tanada cikin nasara kafin a yi la’akari da ba su aikin.
FRSC ta buƙaci jama’a da masu amfani da kafafen sada zumunta da su yi watsi da wannan labari, tare da gujewa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba, musamman ikirarin cewa an raba guraben aikin ga wasu mutane, mazabu ko muradun siyasa.
#NexviewTV #FRSC #FRSCRecruitment2026 #FRSCRecruitment #NigeriaNews #GombeState #RecruitmentNews #BreakingNews #NewsUpdate #NigeriaRecruitment #RoadSafety #NigeriaNewsUpdate
Comments
Post a Comment