Gwamnan Katsina Ya Yabi Sojoji Kan Dakile Harin Masu Garkuwa da Mutane


 


Gwamnan Katsina Ya Yabi Sojoji Kan Dakile Harin Masu Garkuwa da Mutane


Umar Nusaiba Ibrahim 


Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, ya yaba wa dakarun Rundunar Sojin Najeriya bisa dakile yunkurin ’yan ta’adda na kai hari da yin garkuwa da dimbin mazauna yankin Gidan Iyado da ke Karamar Hukumar Bakori ta jihar.


Gwamnan ya kuma yaba wa jami’an Hukumar DSS da ’yan sa-kai bisa bayanan sirrin da suka taimaka wajen gudanar da samamen, wanda ya kai ga hallaka ’yan ta’adda 18 tare da kwato bindigogi, harsasai, babura da dabbobin da aka sace.


Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Gida na jihar, Nasir Mua’su, ya ce aikin sojojin ya samu nasara ne sakamakon sahihan bayanan sirri game da shirin ’yan ta’addan na yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.


Ya ce ’yan ta’addan na karkashin jagorancin wani Alhaji Musa Duki, tsohon shugaban makaranta da ya koma jagoran ’yan bindiga, wanda ke gudanar da ayyukansa daga dajin Mununu a Karamar Hukumar Faskari. An kwato bindigar G3 guda daya, AK-47 guda biyu, harsasai 14, babura uku, shanu biyu da tumaki 94.


A wani bangare kuma, Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta sun ci gaba da gudanar da ayyukan yaki da ta’addanci da garkuwa da mutane a jihohin Kaduna, Katsina, Kebbi da Sokoto, inda aka samu nasarori da dama tsakanin ranar 11 zuwa 17 ga Satumba 2026.


A cikin ayyukan, sojoji sun kubutar da mutane da dama da aka yi garkuwa da su, tare da kama wasu da ake zargi da hada kai da ’yan ta’adda da kuma masu kai musu bayanai. A Sokoto, an kuma kai samame wani wurin da ake zargin maboyar kungiyar Lakurawa ce.


A yankin Arewa maso Gabas, dakarun Operation HADIN KAI sun kubutar da mutane 14 a Borno, ciki har da Limamin Garin Ngoshe, Malam Sadiq, wanda aka yi garkuwa da shi tun ranar 3 ga Maris 2026. An kuma kama wasu da ake zargin ’yan kungiyar masu garkuwa da mutane ne a Jihar Adamawa.


Haka kuma, a Arewa ta Tsakiya, sojojin Operation Savannah Shield da Operation WHIRL STROKE sun gudanar da samame a jihohin Niger, Kwara, Benue, Kogi da Taraba, inda aka kashe wasu ’yan ta’adda, aka kwato makamai tare da kubutar da mutane 22 da aka yi garkuwa da su a Jihar Niger.


A nasa bangaren, Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya yaba wa dakarun bisa jajircewa da sadaukarwar da suke nunawa wajen yakar ’yan ta’adda, kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su da kuma dakile hanyoyin samun makamai da bayanan sirri.


Oluyede ya bukaci sojojin da kada su sassauta wajen gudanar da ayyukansu, tare da jaddada cewa Rundunar Sojin Najeriya za ta ci gaba da ayyukan har sai an tabbatar da zaman lafiya da tsaro a sassan kasar.


#NexViewTV #Katsina #DikkoRadda #NigerianArmy #Military #OperationFANSANYAMMA #OperationHADINKAI #Security #Terrorism #Kidnapping #Banditry #Sokoto #Kaduna #Kebbi #Borno #Niger #Kwara #Benue #Kogi #Taraba #Nigeria #BBCHausa #Arewa24 #ArewaRadio #RFIHausa #DailyTrust #HausaNews

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING