Gwamnati Ta Mayar Da Tantance Matsayin Manyan Makarantu Tilas
Gwamnati Ta Mayar Da Tantance Matsayin Manyan Makarantu Tilas
Umar Nusaiba Ibrahim
Gwamnatin Tarayya ta mayar da shiga cikin tsarin tantance matsayin manyan makarantu a Najeriya ya zama tilas ga jami’o’i, polytechnics da kwalejojin ilimi. Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taro da kwamitin kula da tantance matsayin manyan makarantu.
Alausa ya ce faɗaɗa tsarin zai taimaka wajen inganta inganci, rikon amana da ayyukan makarantun gaba da sakandare, tare da ƙarfafa gasa mai amfani tsakaninsu. Ya ce tsarin zai bai wa makarantu damar sanin ƙarfinsu da wuraren da suke buƙatar gyara.
Ministan ya bayyana cewa za a fara tantance jami’o’i na shekarar 2026/2027 a watan Satumba, yayin da za a tsara lokacin da za a fara aikin tantance polytechnics da kwalejojin ilimi. Ya kuma ce gwamnati za ta samar da ƙa’idojin da za su tabbatar da cewa dukkan shugabannin manyan makarantu sun shiga tsarin.
A cewar Alausa, shirin na daga cikin sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa a fannin ilimi, kuma Ma’aikatar Ilimi za ta samar da tallafin kuɗi, manufofi da horo domin tabbatar da sahihancin tsarin.
Shugaban kwamitin, Farfesa Peter Okebukola, ya ce faɗaɗa tsarin zuwa polytechnics da kwalejojin ilimi zai taimaka wajen samar da ma’aunin tantance ingancin manyan makarantu baki ɗaya. Ya ce hakan zai ƙara bai wa makarantun Najeriya damar inganta matsayinsu da yin gogayya da manyan makarantu na duniya.
#Education #NigeriaEducation #TertiaryEducation #Universities #Polytechnics #CollegesOfEducation #FG #EducationReform #NigerianUniversities

Comments
Post a Comment