Gwamnati Za Ta Bai Wa ‘Yan Kasuwa Dalibai Naira Miliyan 50
Gwamnati Za Ta Bai Wa ‘Yan Kasuwa Dalibai Naira Miliyan 50
Umar Nusaiba Ibrahim
Gwamnatin Tarayya ta buɗe shafin neman tallafin kuɗi ga ɗaliban da ke gudanar da harkokin kasuwanci, inda za ta bai wa wasu 50 daga cikinsu tallafin da zai kai Naira miliyan 50 ga kowane ɗan kasuwa. Shirin mai suna Student Venture Capital Grant, wanda aka fi sani da Next Moonshot Initiative, ya fi mayar da hankali kan ɗaliban da ke da sabbin dabarun kasuwanci da suka shafi Kimiyya, Fasaha, Injiniyanci da Lissafi (STEM).
Mai kula da shirye-shirye na musamman a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Adebayo Onigbanjo, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a. Ya ce gwamnati na neman ƙwararrun ɗalibai masu sabbin dabaru daga sassan ƙasar, inda daga cikin waɗanda za su nemi tallafin za a zaɓi kamfanoni ko harkokin kasuwanci 50 da suka fi fice.
Onigbanjo ya bayyana cewa waɗanda suka yi nasara za su samu tallafin da bai haɗa da mayar da kuɗi ba, wanda zai kai Naira miliyan 50, domin bunƙasa da faɗaɗa kasuwancinsu. Ya ce shirin na daga cikin manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Tinubu, tare da kasancewa wani ɓangare na shirin farfaɗo da fannin ilimi na ƙasa, musamman ɓangaren STEM.
Ya ƙara da cewa za a fara tantance aikace-aikacen ne ta hanyar amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI), kafin ƙwararrun masu tantancewa guda 10 su gudanar da cikakken bincike. Waɗanda za su tsallake matakin farko za su gabatar da ayyukansu ta yanar gizo, sannan waɗanda suka kai matakin ƙarshe za su halarci sansanin horaswa na tsawon kwanaki uku tare da gabatar da harkokinsu a gaban kwamitin tantancewa. Wadanda suka yi nasara kuma za su samu jagoranci da shawarwari na tsawon watanni shida.
A wani mataki na ƙara wayar da kan ɗalibai, tawagar shirin da abokan haɗin gwiwa za su gudanar da rangadin neman masu neman tallafin a jami’o’i da sauran manyan makarantun gaba da sakandare daga 6 zuwa 30 ga Satumba 2026. Za a ziyarci makarantu tara a shiyyoyin siyasa shida na ƙasar, ciki har da Jami’ar Bayero da ke Kano da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano, yayin da za a kuma kafa tsarin Campus Ambassador a wasu makarantu 20. An bayyana cewa wa’adin karɓar aikace-aikacen zai ƙare a 30 ga Satumba, 2026.
Hashtags:
#NexviewTV #Nigeria #GwamnatinTarayya #StudentEntrepreneurs #NextMoonshot #StudentVentureCapitalGrant #Tallafi #STEM #Matasa #Ilimi #Kasuwanci #Innovation #Entrepreneurship

Comments
Post a Comment