Gwamnatin Kwara da PDP Sun Yi Sa-in-Sa Kan Cire Allunan Kamfen
Gwamnatin Kwara da PDP Sun Yi Sa-in-Sa Kan Cire Allunan Kamfen
Samira Ahmad Danketa
Sabuwar takaddama ta siyasa ta kunno kai a Jihar Kwara bayan cire allunan kamfen na ɗan takarar gwamnan PDP, Injiniya Suleiman Bolakale Kawu, daga wasu wurare a Ilorin.
Gwamnatin jihar ta ce cire allunan na daga cikin matakan tabbatar da bin dokokin tallace-tallace da allunan sanarwa. Sai dai PDP ta zargi gwamnatin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da amfani da hukumomin gwamnati wajen takura wa ’yan adawa da cire kayan kamfen ɗinsu.
Babban Manajan Hukumar KWASAA, Toba Adeyeye, ya musanta cewa an yi wa PDP ko wani ɗan takara na musamman, inda ya ce hukumar tana aiwatar da doka ne ba tare da nuna bambanci ba. Ya kuma ce an cire wasu allunan saboda rashin samun izini da kuma zargin lalata ababen more rayuwa.
Adeyeye ya ƙara da cewa hukumar ta taɓa cire allunan kamfen na ’yan APC da suka karya doka a lokacin zaɓen fidda gwani. Ya buƙaci dukkan ’yan siyasa su bi ƙa’idojin da aka gindaya, yana mai cewa “kamfen zai zo ya wuce, amma jihar Kwara za ta ci gaba da kasancewa.”
Shi kuwa Kawu ya ce cire sunansa daga allon talla ba zai cire burinsa na yi wa al’ummar Kwara hidima ba. PDP ta kuma yi kira ga Gwamna AbdulRazaq da ya dakatar da abin da ta kira takura wa ’yan adawa, tare da ba su damar gudanar da harkokin siyasa cikin ’yanci.
#KwaraState #KwaraPolitics #PDP #APC #Ilorin #SuleimanKawu #AbdulRahmanAbdulRazaq #KWASAA #2027Election #NigeriaPolitics #PoliticalNews #HausaNews #NewsUpdate #KwaraNews

Comments
Post a Comment