Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi Da Ikirarin Obi Da Kwankwaso Kan Nasarar Tinubu A 2027
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi Da Ikirarin Obi Da Kwankwaso Kan Nasarar Tinubu A 2027
Umar Nusaiba Ibrahim
Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da ikirarin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da mataimakinsa, Sanata Rabiu Kwankwaso, cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya ce jam’iyyar APC na da cikakken yaƙinin cewa za ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasa da kuma sauran muƙaman zaɓe a Jihar Kaduna.
Rabi’u Musa ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV a ranar Alhamis, inda ya yi watsi da ra’ayin cewa ana samun karuwar adawa da APC da Shugaba Tinubu a yankin Arewa. Ya ce wannan ra’ayi ne kawai na wasu mutane, yana mai cewa APC za ta yi nasara a Kaduna a zaɓen 2027, ciki har da zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna da sauran kujerun zaɓe.
A nasa ɓangaren, Peter Obi ya yi kira ga magoya bayansa da su kasance cikin shiri domin kare ƙuri’unsu a rumfunan zaɓe, yana mai cewa ba za a sake samun damar tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a kamar yadda ya yi zargin an yi a zaɓen 2023 ba. Obi ya ce masu ƙoƙarin sauya sakamakon zaɓe ta hanyar tsarin IReV na Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, za su fuskanci ƙalubale, yana mai cewa magoya bayansa za su tabbatar da cewa ƙuri’unsu sun ƙirga.
Shi ma Rabiu Kwankwaso ya ce Najeriya na buƙatar shugaba mai ƙwarewa, ƙarfi da jajircewa wajen magance matsalolin ƙasar. Ya gargadi ’yan Najeriya da kada su sake yin kuskure wajen zaɓar shugabanni, tare da yin nuni da cewa kasancewar jam’iyya mai mulki na da gwamnoni sama da 30 ba ya tabbatar da samun nasara a zaɓe. Ya kawo misalin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, wanda ya sha kaye a zaɓen 2015 duk da kasancewarsa shugaban ƙasa mai ci.
Sai dai Sakataren Jam’iyyar APC na Ƙasa, Ajibola Basiru, ya bayyana kalaman Obi da Kwankwaso a matsayin zance marar tushe da buri kawai. Ya tunatar da su cewa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya taɓa samun nasarar sake zaɓe a lokacin da yake kan mulki. A halin da ake ciki kuma, jam’iyyar ADC a Jihar Rivers ta yi watsi da ikirarin Ministan Abuja, Nyesom Wike, na cewa zai tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a jihar, inda ta ce za ta ci gaba da yaƙin neman zaɓe domin samun nasara a zaɓen 2027.
#Tinubu2027 #APC #PeterObi #Kwankwaso #2027Zabe #NigeriaPolitics #Tinubu #APC2027 #NDC #ADC #Kaduna #Rivers #Nigeria #Zaben2027 #SiyasarNigeria #NexviewTV

Comments
Post a Comment