Gwamnonin Arewa Sun Bukaci Bincike Kan Mutuwar Masu Hakar Ma’adinai 37 a Neja

 Gwamnonin Arewa Sun Bukaci Bincike Kan Mutuwar Masu Hakar Ma’adinai 37 a Neja


Samira Ahmad Danketa 


Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya (NNGF) ta yi kira da a gudanar da cikakken bincike mai gaskiya da adalci kan mutuwar mutane 37, waɗanda suka rasu a lokacin da suke tsare a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Neja.


A cikin wata sanarwa da Gwamnan Jihar Gombe kuma Shugaban ƙungiyar, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya fitar a madadin sauran gwamnonin a ranar Juma’a, ya bayyana mutuwar mutane da yawa, musamman a lokacin da suke tsare, a matsayin abin da ke matuƙar tayar da hankali da damuwa.


Gwamna Yahaya ya bukaci hukumomin da abin ya shafa su gano hakikanin abin da ya faru kafin, lokacin da kuma bayan kama waɗanda abin ya shafa. Ya ce ya kamata binciken ya gudana yadda ya kamata ba tare da katsalandan ba, domin a gano gaskiyar lamarin.


Ya kuma miƙa ta’aziyyar NNGF ga gwamnatin Jihar Neja, al’ummar jihar da kuma iyalan mamatan, yana mai bayyana lamarin a matsayin mummunan bala’i da ya shafi ƙasa baki ɗaya. Ya jaddada cewa rayuwar kowane ɗan Adam tana da daraja, kuma dole ne a mutunta ta tare da kare haƙƙin mutum kamar yadda doka ta tanada.


Gwamnan ya yaba da matakin hukumomin da suka fara bincike, tare da kira da a gudanar da binciken cikin gaskiya da cikakken bayani. Ya kuma yi kira ga jama’a da iyalan waɗanda abin ya shafa da su kasance cikin natsuwa da haƙuri, domin a samu adalci da kuma amsoshin tambayoyin da suka taso. Ya roƙi Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu.


#NexviewTV #NNGF #NigerState #NorthernNigeria #Miners #NSCDC #BreakingNews #NigeriaNews #Investigation #Justice #Accountability #NewsUpdate #Arewa #NigerNews #HausaNews

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING