Hanga, Gaya, Doguwa da wasu fitattun ’yan siyasa sun koma APC a Kano


 

Hanga, Gaya, Doguwa da wasu fitattun ’yan siyasa sun koma APC a Kano


Umar Nusaiba Ibrahim 


Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta karɓi wasu fitattun ’yan siyasa da magoya bayansu da suka sauya sheƙa daga wasu jam’iyyun siyasa zuwa cikinta. Daga cikin waɗanda suka koma jam’iyyar akwai Sanata Rufa’i Sani Hanga, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa, tare da wasu mutane 136,038.


An karɓi sabbin mambobin ne a ranar Asabar, yayin wani taron ƙaddamar da ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Jihar Kano, gabanin babban zaɓen 2027.


Cikin sauran fitattun mutanen da suka koma APC akwai mataimakin shugaban jam’iyyar NDC a Kano, Ali Datti Yako, da wasu shugabannin jam’iyyar a jihar. Haka kuma, tsohon shugaban Ƙaramar Hukumar Ungogo, Badaru Umar, da wasu magoya bayan tsohon ɗan takarar gwamnan Kano na APC a zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, sun sauya sheƙa zuwa APC.


Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Isyaku Ali Danja, shi ma ya koma APC tare da magoya bayansa. Sauran waɗanda suka shiga jam’iyyar sun haɗa da tsohon ɗan takarar mataimakin gwamnan Kano na PDP, Yusuf Bello Danbatta, da tsohuwar mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara ta musamman, Sanata Baraka Sani.


Haka kuma, shugaban wani tsagin NNPP, Abdullahi Zubairu Abiya, tsohon ɗan takarar Sanatan NNPP, Abdulmajid Dauda Dandawaki, da ɗan takarar majalisar dokokin Jihar Kano na NDC, Kabiru Adamu Kofar Ruwa, na cikin waɗanda suka koma APC. Ana ganin wannan sauya sheƙa zai ƙara wa APC ƙarfi yayin da siyasar Kano ke ci gaba da sauyawa gabanin zaɓen 2027, musamman bayan komawar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar.



#APC #Kano #SiyasarKano #Zaben2027 #Tinubu #RufaIHSaniHanga #KabiruGaya #Doguwa #NNPP #NDC #PDP #SauyaSheka #KanoPolitics #NigeriaPolitics #NexviewTV #BBCHausa 

#Arewa24 #Arewaradio #RFIHausa

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING