Ilimi Ba Yaudara Ba Ne — Sanata Ya Gargadi Dalibai
Ilimi Ba Yaudara Ba Ne — Sanata Ya Gargadi Dalibai
Umar Nusaiba Ibrahim
Sanata Shuaib Afolabi Salisu, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Fasahar Sadarwa da Tsaron Intanet, ya bukaci daliban Najeriya da su rungumi ilimi tare da jajircewa, yana mai bayyana ilimi a matsayin hanyar samun ci gaba da kuma taka muhimmiyar rawa a cikin al’umma.
Salisu, wanda ke wakiltar Ogun ta Tsakiya, ya yi Allah-wadai da yadda wasu matasa ke cewa “ilimi yaudara ne”, inda ya ce ilimi ya taimaka wajen samar da manyan maza da mata da dama a cikin al’umma, musamman a Jihar Ogun.
Sanatan ya ce shawarar da iyayensa suka ba shi shekaru 46 da suka gabata ce ta kara masa sha’awar neman ilimi. Ya kuma bayyana cewa bayan rasuwar mahaifiyarsa, ya fahimci cewa ilimi ne hanyar da za ta ba shi damar zama mai amfani a cikin al’umma.
Salisu ya bayyana hakan ne a wajen shirin tallafawa ilimi na shekara-shekara na SAS Omoyayi Educational Support Programme, wanda aka gudanar a June 12 Cultural Centre da ke Kuto, Abeokuta, karkashin taken “Zuba Jari a Ilimi, Karfafa Shugabannin Gobe.”
Sanatan ya sake jaddada kudirinsa na tallafawa ilimi, ilimin fasahar zamani da kuma koyar da dabarun ICT, inda ya bukaci daliban da su dauki kansu a matsayin shugabannin gobe, har ma da Sanatoci. Ya ce yanzu suna da damar samun ingantattun makarantu da kuma misalan mutanen da za su yi koyi da su.
Ya ce: “Ku mayar da hankali kan karatunku. Idan kun tabbatar cewa abin da kuke yi shi ne daidai, kada ku ji tsoron bambanta da wasu. Ku ci gaba da yin abin da ya dace. Ilimi shi ne hanya ta ci gaba da kuma kasancewa cikin al’umma.”
A nasa bangaren, Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar Ogun, Farfesa Abayomi Arigbabu, ya tabbatar da kudirin gwamnatin Dapo Abiodun na inganta harkar ilimi a jihar.
Shi ma Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ogun, Oludaisi Elemide, ya kwatanta tallafin da aka bai wa daliban da shuka iri, yana mai cewa za a fahimci amfaninsa ne idan yaran suka girma suka zama manyan mutane a nan gaba.
Shugaban kungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Ogun, Comrade Noah Sewakanu, ya bukaci daliban da su yi amfani da kayan karatun da aka raba musu yadda ya kamata, tare da dagewa wajen karatu domin cimma burinsu da kuma zama jakadun kwarai na jihar.
#Education #Ilimi #Nigeria #NigerianStudents #EducationIsNotAScam #OgunState #Students #YouthDevelopment #DigitalLiteracy #ICT #Empowerment #FutureLeaders #SASOmoyayi #SenatorSalisu #NUT #NexViewTV #Arewa #Arewa24 #BBCHausa #ArewaRadio #RF Hausa #RFIHausa
Comments
Post a Comment