INA SHUGABAN NAJERIYA? — PETER OBI YA TAMBAYI TINUBU KAN RASHIN BAYYANARSA
INA SHUGABAN NAJERIYA? — PETER OBI YA TAMBAYI TINUBU KAN RASHIN BAYYANARSA
Umar Nusaiba Ibrahim
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya nuna damuwa tare da neman ƙarin bayani kan inda Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, yake, sakamakon tsawon lokacin da bai bayyana a bainar jama’a ba.
Obi, wanda tsohon gwamnan Jihar Anambra ne, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, wadda mai magana da yawunsa, Idris Zekeri Jnr, ya fitar.
Rahotanni sun ce Shugaba Tinubu ya bar Najeriya ranar 30 ga Agusta, 2026, domin gudanar da hutun aiki na makonni uku a Turai, kamar yadda fadar shugaban ƙasa ta bayyana. Sai dai wasu ‘yan adawa da ƙungiyoyin farar hula sun fara nuna damuwa bayan lokacin da aka yi tsammanin zai dawo ya wuce.
Obi ya yi wannan tsokaci ne bayan jawabin da Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ya gabatar a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 (UNGA) da aka gudanar a birnin New York. Ya kwatanta halartar Ghana da kasancewar Najeriya a taron, yana tambayar dalilin da ya sa Tinubu bai halarci tarukan UNGA na baya-bayan nan ba.
Ya ce duk da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa New York, hakan bai kawar da tambayar da ake yi kan inda Shugaban Ƙasar yake ba, musamman a lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da tsaro.
Obi ya ce: “Ina Shugaban Najeriya, musamman a lokacin da ƙasar ke fuskantar manyan ƙalubale a cikin gida da kuma wajen ƙasa?” Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da addu’ar samun dawowar shugaban ƙasar da kuma jagorancin da zai taimaka wajen magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
#NexViewTV #PeterObi #Tinubu #Nigeria #NDC #UNGA #KashimShettima #NigeriaPolitics #HausaNews #Arewa #ArewaNews #Arewa24 #BBCHausa #RFIHausa #ArewaRadio #FreedomRadioKano #DailyTrust #LabaranArewa #LabaranDuniya #HausaNewsUpdate

Comments
Post a Comment