Iyalan El-Rufai Sun Bai Wa Ministan Tsaro Kwana 7 Ya Janye Zargin Kisan Kudancin Kaduna
Iyalan El-Rufai Sun Bai Wa Ministan Tsaro Kwana 7 Ya Janye Zargin Kisan Kudancin Kaduna
Umar Nusaiba Ibrahim
Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, sun bai wa Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), wa’adin kwanaki bakwai da ya gabatar da hujjar da ke tabbatar da zargin cewa El-Rufai ya shirya kisan mutane a Kudancin Kaduna, ko kuma ya janye zargin tare da ba da haƙuri a bainar jama’a.
Janar Christopher Musa ya yi wannan zargi ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar 3 ga Satumba. Ministan ya ce gwamnatin El-Rufai tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023 ta ƙara raba kan al’ummar Kaduna, yana mai cewa lamarin tsaro a lokacin ya kasance cikin wani yanayi mai tsanani.
Musa ya kuma ce al’ummar Kudancin Kaduna ba za su iya farin ciki da mutumin da ya yi zargin cewa ya shirya kisan mutanensu da gangan ba. Ya ƙara zargin tsohon gwamnan da rusa gidajen wasu mutane da ya samu saɓani da su. Sai dai iyalan El-Rufai sun musanta waɗannan zarge-zarge, suna mai cewa ba a gabatar da wata hujja da za ta tabbatar da su ba.
A cikin wata sanarwa da ɗan fari na tsohon gwamnan, Hon. Mohammed Bello El-Rufai, ya sanya wa hannu, iyalan sun ce zargin na da matuƙar nauyi, kuma suna da haƙƙin neman a tabbatar da shi da ingantattun hujjoji. Sun bukaci Ministan Tsaron da ya yi amfani da kafar da ya yi zargin wajen janye kalaman nasa tare da ba da cikakken haƙuri.
Iyalan sun ce idan Janar Musa bai gabatar da hujja ko ya janye zargin cikin kwanaki bakwai ba, za su ɗauki matakan shari’a da suka dace domin kare martabar tsohon gwamnan. El-Rufai, wanda ya taɓa zama Ministan FCT da kuma Gwamnan Kaduna, a yanzu yana cikin jagorancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
#ElRufai #ChristopherMusa #Kaduna #SouthernKaduna #NigeriaPolitics #ADC #PoliticsToday #ChannelsTV #NexviewTV #Arewa24 #RFIHausa #BBCHausa #HausaNews #LabaranHausa

Comments
Post a Comment