JAMB Ta Saki Sakamakon UTME na 2026 ga Ƴan Ƙasa da Shekaru 16
JAMB Ta Saki Sakamakon UTME na 2026 ga Ƴan Ƙasa da Shekaru 16
Daga Zamira Ahmad Nasidi
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Najeriya (JAMB) ta fitar da sakamakon 2026 (UTME) na ƴan takarar da ba su kai shekara 16 ba.
Mai ba (JAMB) shawara kan hulɗa da jama’a, Dr Fabian Benjamin, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Asabar.
Sai dai hukumar ta jaddada cewa fitar da sakamakon ba yana nufin ƴan takarar za su samu damar shiga jami’a kai tsaye ba. A cewar (JAMB), ƴan takarar da za a yi wa la’akari da su dole ne su cika wasu ƙa’idoji na musamman.
JAMB ta bayyana cewa ɗan takarar da ake ɗauka a matsayin underage shi ne wanda zai kasance ƙasa da shekara 16 zuwa ranar 30 ga Satumba 2026.
An fitar da sakamakon ne domin ƴan takara da iyayensu ko masu kula da su su san yadda suka yi jarabawar. Amma ba za a iya amfani da sakamakon wajen neman admission ba, sai ga waɗanda suka cika dukkan sharuɗɗan da hukumar ta gindaya.
Daga cikin muhimman sharuɗɗan akwai samun aƙalla maki 320 a (UTME), tare da samun 80% ko sama da haka a darussan SSCE da suka dace, da kuma cika sauran buƙatun (Post-UTME) na jami’ar da ɗan takarar ya zaɓa.
Hukumar ta kuma ce ƴan takarar za su fuskanci ƙarin tantancewa kafin a yanke hukuncin ƙarshe. Wannan tsari bai kammala ba, musamman saboda ana jiran sakamakon NECO domin kammala tantance wasu daga cikin ƴan takarar.
JAMB ta gargadi iyaye da ƴan takara da su yi hattara da masu ikirarin cewa za su iya samar da admission ga ƴan ƙasa da shekaru 16 ta hanyar da ba ta hukuma ba.
Hukumar ta sake jaddada cewa yin UTME da samun sakamako ba tabbacin samun admission ba ne, musamman ga ƴan takarar da ba su kai shekarun da doka ta tanada ba.
Yadda za a duba sakamako: Ɗan takara zai iya aika kalmar (RESULT )zuwa 55019 ko 66019 daga lambar wayar da ya yi amfani da ita wajen rajistar (UTME).
#JAMB #UTME2026 #JAMB2026 #JAMBResult #UTMEResult #UnderageCandidates #JAMBAdmission #Admission2026 #JAMBNews #EducationNews #NigeriaEducation #NigeriaStudents #NECO #PostUTME #UniversityAdmission #Students #EducationNigeria #NigeriaNews #LabaranNigeria #ZamiraAhmadNasidi #AdmissionNews

Comments
Post a Comment