Jami’ar EKSU Ta Bukaci Sabbin Ɗalibai Su Rungumi Ladabtarwa da Nagarta


 

Jami’ar EKSU Ta Bukaci Sabbin Ɗalibai Su Rungumi Ladabtarwa da Nagarta


Umar Nusaiba Ibrahim 


Jami’ar Ekiti State University (EKSU), Ado-Ekiti, ta bukaci sabbin ɗaliban shirin Sandwich da aka karɓa su ɗauki rantsuwar matriculation ɗinsu a matsayin alkawarin bin dokokin jami’a, ladabtarwa, gaskiya da kuma zama ’yan ƙasa nagari.


Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Babatola Ayodele, wanda Mataimakin Shugaban Jami’ar mai kula da harkokin ilimi, Farfesa Williams Adebayo, ya wakilta, ya ce an ba ɗaliban guraben karatu ne saboda jami’ar ta ga suna da damar yin nasara. Ya bukace su da su mayar da wannan dama zuwa nasara ta hanyar jajircewa, aiki tuƙuru da azama.


Ayodele ya bayyana haka ne a wajen bikin matriculation na shekarar 2026 na sabbin ɗaliban shirin Sandwich, wanda aka gudanar a harabar jami’ar da ke Moba Grammar School, Otun-Ekiti. Ya tunatar da su cewa shiga jami’a ba ƙarshen tafiya ba ne, illa farkon wata sabuwar tafiya ce da abin da za su yi da damar da aka ba su zai ƙayyade irin nasarar da za su samu.


Ya kuma shawarci ɗaliban da kada su bari ƙalubalen karatu, ayyukan gida, jarabawa da sauran nauyin da ke kansu ya karya musu gwiwa. Ya ce su yi amfani da kwarewar da suka samu a wuraren aikinsu da kuma hulɗarsu da al’umma wajen ƙara inganta karatunsu. Ya kuma bukace su da su mayar da nagarta, gaskiya da ɗaukar nauyi ginshiƙan tafiyarsu ta ilimi.


A nasa jawabin, Oore na Otun-Ekiti, Oba Adekunle Adeagbo, ya taya sabbin ɗaliban murna tare da bukatar su mayar da hankali kan karatunsu, su guji duk wani abu da zai iya raba hankalinsu ko kawo cikas ga burinsu. Jami’ar ta kuma yaba da haɗin kan sarautar gargajiya, al’ummar Otun-Ekiti da Moba Grammar School wajen tallafa wa ayyukan jami’ar.


#EKSU #Education #SandwichProgramme #Matriculation #Students #AcademicExcellence #Discipline #NigeriaEducation #HausaNews #NexviewTV #Arewa24 #RFIHausa #BBCHausa

Comments

Popular posts from this blog

Gunshots As Rival Cult Groups Clash At Rivers Varsity

17 Bandits, 10 Police Officers Killed In Zamfara-Kebbi Clash

KANO BRIDE SENTENCED TO DEATH BY HANGING 9 DAYS AFTER WEDDING